Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta naɗa Éric Sékou Chelle a matsayin babba kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya, Super Eagles.
Wata sanawar da hukumar ta fitar a shafukanta na sada zumunta, ta ce ta yi naɗin ne bisa shawara daga wani kwamitinta.
“A zamansa da aka yi a Abuja ranar Alhamis 2 watan Janairun shekarar 2025, kwamiti kan dabaru da ci-gaba ya ba da shawarar naɗa tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafar Mali a matsayin sabon kocin Super Eagles. Kwamitin zartarwa na hukumar NFF ya amince da shawarar ranar 7 ga watan Janairu,” in ji sanarwar.
“Chelle, ya yi wa tawagar Aiglons ta Mali jagoranci a wasanni biyar baya ga kasancewa kocin kulob-kulob kamar su GS Consolat da FC Martigues da Boulogne da kuma MC Oran, ya jagoranci tawagar Aiglons tun shekarar 2022,” a cewar NFF.
Mali ta kusa da samun gurbi a matakin dab da na ƙarshe a gasar AFCON ta shekarar 2023 da aka yi inda Cote d’Ivoire ta doke Mali da 2-1.
Cote d’Ivoire ce dai ta lashe kofin AFCON na gasar 2023 bayan ta doke Nijeriya a wasan ƙarshe na gasar da aka yi a filin wasan Alassane Ouattara a Abidjan.
“Kocin mai shekara 47 ya murza leda a Martigues da Valenciennes da Lens da Istres da kuma Chamois Niortais a Faransa a lokacin da yake ɗan wasa,” in ji sanarwar.
NFF ta ba shi alhaƙin kai Super Eagles gasar Kofin Duniya ta 2026 kuma za a ci gaba da buga wasannin neman shiga gasar ne a watan Maris.
Wannan shi ne kusan karon farko da tawagr Super Eagles za ta samu koci ɗan Afirka da ba Nijeria ba.