Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta cim ma yarjejeniya da mai horar da ‘yan wasan ƙasar Jamus, Bruno Labbadia domin ya jagoranci ƙungiyar Super Eagles.
NFF ta sanar da naɗin ɗan ƙasar Jamus ɗin ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a safiyar ranar Talata, kana babban sakataren hukumar Mohammed Sanusi ya tabbatar da naɗin yana mai cewa sabon kocin zai soma aiki ne nan-take.
“Kwamitin zartaswa na hukumar NFF ya amince da shawarar kwamitinsa kan fasaha da ci gaba na naɗa Mista Bruno Labbadia a matsayin babban kocin Super Eagles kana aikinsa zai kankama a nan-take,” in ji Sanusi.
An haifi Labbadia ne a Darmstadt da ke ƙasar Jamus a ranar 8 ga watan Fabrairu 1966, sabon kocin, ya taba ci wa Die Mannschaft wasa har sau biyu.
Sunayen da aka fi sanin Kocin da su a yanzu sune, Hertha Berlin da VfB Stuttgart sai kuma a baya an fi saninsa da VfL Wolfsburg da Hamburger SV da Bayer Leverkusen, da dai sauransu, sannan yana da lasisin ƙwarewa a UEFA.
Babban ƙalubalen da ke gaban Labbadi a yanzu shi ne yadda zai jagoranci zakarun Afirka har sau uku a wasanni biyu na neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na shekarar 2025 da Jamhuriyar Benin a ranar Asabar 7 ga Satumban garin Uyo da kuma ƙasar Rwanda a ranar Talata, 10 ga watan Satumban a birnin Kigali, tare da sauran wasanni huɗu da za a buga don kammala wasannin share-fage da za a yi a cikin watannin Oktoba da Nuwamba.