Neymar ya kafa tarihi a matsayin dan wasa da ya fi tsada a lokacin da ya koma PSG kan kudi dala miliyan 241 a shekarar 2017:Hoto/Anadolu Images

Paris St-Germain ta amince ta sayar da dan wasan Brazil Neymar ga kungiyar kwallon kafar Al-Hilal da ke Saudiyya kan kimanin Yuro miliyan 90 (£77.6m) ciki har da tsarabe-tsarabe.

Abin da ya rage kawai shi ne a kammala duba lafiyar dan wasan mai shekara 31 kafin ciniki ya fada.

Neymar, wanda PSG ta saya daga Barcelona a kan yuro miliyan 222 a 2017, bai buga wasan Ligue 1 da kungiyarsa ta yi kunnen-doki da Lorient ranar Asabar ba.

Wata majiya da ke kusa da PSG ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa Neymar, "ba shi da gurbi" a shirin kocin PSG Luis Enrique a kakar wasa ta bana.

An yi wa Neymar aiki a idon sahu a farkon watan Maris, kuma ya koma cikin tawagar PSG ta rangadin shirin kakar wasa da ta yi a Asia a lokacin.

Neymar ya yi fama da raunuka daga lokaci zuwa lokaci a zamansa a PSG.

Duk da cewa ya taimaka wa kulob din ya kai wasan karshe na Gasar Zakarun Turai, ba a saka shi a muhimman wasannin kungiyar.

Neymar zai bi sahun jerin manyan ‘yan wasan da suka koma kasar mai arzikin man fetur tun bayan da Cristiano Ronaldo ya koma Al-Nassr a watan Janairu.

Al-Hilal ta dade da kasancewa daya daga cikin manyan kulob din Saudiyya kuma ta dauki kofin Gasar Zakarun Asia sau hudu.

TRT Afrika da abokan hulda