Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ya san ‘yan wasan Arsenal za su yi ta kai wa kungiyarsa hare-hare a fafatawar da za su yi ranar Laraba.
Da yake hira da manema labarai ranar Talata, Guardiola ya ce zai rika sauya badaru daga farkon wasan zuwa karshe saboda ya san salon wasan da Arsenal ta shirya musu.
Maki biyar ne ke tsakanin Arsenal da ke saman teburin gasar Firimiya da Man City da ke biye da ita.
Man City na da kwantan wasa biyu.
Pep Guardiola ya tabbatar da cewar karawar City da Arsenal ba za ta zo da sauki ba.
“Tun da ma Arsenal tana aiki tukuru wajen rike kwallo, ‘yan wasan da ake zaba wa kulob din suna da inganci da kwarewa. Mikel (Arteta) ya kawo su wani mataki na daban,” a cewar Guardiola.
Sai dai ya ce ‘yan wasan City za su yi kokarin samun makin da ya dace a karawar.
A kan abotarsa da kocin Arsenal, Guardiola ya ce har yanzu su aminai ne.
“Babu abin da ya sauya kan yadda nake ji game da shi. Ba ma magana sosai yanzu saboda mu abokan hamayya ne.”