Kocin Roma, Jose Mourinho, ya soki ‘yan kulob dinsa kan rashin saka jiki a wasa a karawarsu da Servette da suka tashi 1-1.
Romelu Lukaku ne ya fara zura wa kungiyar Roma kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci, sai dai kuma Chris Bedia ya rama wa Servette bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Canjaras din da aka tashi a wasan ya sa Roma tana mataki na biyu yayin da Slavia Prague da ke saman teburin a gasar Europa ta fi su da maki biyu.
"Da alama wasu da ba su saba wasa a Gasar Turai ba sun buga wasan sama-sama," in ji Mourinho.
"Ni ban gane ba. Na yi wasanni 150 a Gasar Zakarun Turai da suka fi wannan muhimmanci kuma na yi matukar mayar da hankalin kan wasannin nan.
"Kuma wasu ‘yan wasan ne kawai suke mayar da hankali na tsawon minti 90, kuma ba sai na fadi sunayensu ba. Akwai wasu kuma wadanda basa saka jiki a irin wannan wasan."
Roma na bukatar doke Sheriff Tiraspol a wasansu na karshe a matakin rukuni tare da fatan cewar Slavia Prague ba za ta doke Servette ba domin samun damar dare saman teburin rukuni kuma su samu damar zuwa mataki na gaba nan-take.
Kasancewa na biyu a teburin na nufin sai sun yi wasan raba-gardama da kulob din zai sauko daga Gasar Zakarun Turai.
Mourinho ya ce buga wasan raba-gardama ba zai kasabce wata masifa ba, amma ya dora wa wasu ‘yan wasansa alhakin rasa damar samun maki uku a wasan da suka yi kasar Switzerland.