Shahararren ɗan wasa ɗan asalin Argentina, Lionel Messi, wanda ke buga wasa a Inter Miami ta Amurka, 'yana so ya ƙauracewa' wasan da za su buga da Sporting Kansas City ranar Talata mai zuwa.
Wasan zai gudana ne a gidan Sporting KC da ke jihar Kansas, inda hasashen yanayi ke cewa za a samun tsanantar yanayin sanyi da zai kai -24C a ma'aunin Celcius.
Wasan na gasar Zakarun nahiyar Amurka ne, ƙarƙashin hukumar ƙwallo ta nahiyar, CONCACAF. Wasan shi ne wanda za a buɗe gasar da shi, kuma shi ne ƙafar farko ta wasannin da ƙungiyoyin biyu za su buga a zagaye biyu.
A cewar rahotannin, Messi yana son ya kaucewa buga wasan saboda ya saba da buga wasa a sansanin ƙungiyarsa da ke kudancin jihar Florida, wadda ke da yanayin zafi.
Hasashen masana yanayi ya ce filin da za a yi wasan zai kai awon zafi -15C a ma'aunin Celcius, amma yanayin iska zai sanya a ji kamar ya kai tsaninin har -24C.
Yiwuwar jinkirtawa
Akwai rahotannin da ke cewa ana tattaunawa kan yiwuwar jinkirta wasan ko a sauya filin wasan zuwa yankin da ke da sauƙin sanyi.
A cewar wani ɗan jarida da shafin Goal ya ambato mai suna Franco Panizo, Messi ba ya karsashin zuwa wasan.
Panizo ya wallafa a shafin sada zumunta cewa, “Wasu majiyoyi sun gaya min cewa Lionel Messi ba ya so ya buga wasan na Talata cikin matsanancin sanyi tare da Sporting KC.
"Ko zai je ko ba zai je ba, za a jira a tabbatar, amma akwai yiwuwar Messi ba zai buga wasan buɗe gasar Zakarun CONCACAF ba.”
Wani makusancin Messi kuma abokin wasansa a Miami, Luis Suarez ya taɓa faɗi a baya game da Messi cewa ba ya ƙaunar buga wasa cikin sanyi, “Ya gaya min cewa yana shan wahala sosai cikin sanyi da ƙanƙara.”
A ranar 25 ga Fabrairu ne za a buga zagaye na biyu na wasan a filin wasa na Chase Stadium, wato gidan Inter Miami da ke jihar Florida.