Lionel Messi ya ce da wulaƙanci ya so yi da "ba ma zai je" Hong Kong ɗin ba gaba ɗaya. Hoto: Reuters

Lionel Messi ya ce bai ƙi halartar wani wasa da aka yi a ƙasar Hong Kong mako biyu da suka wuce wanda ya ɓata ran China, don ya ba ta kunya ba.

Magoya bayan ɗan ƙwallon wanda ya lashe Kyautar Ballon d'Or har sau takwas, sun girmama shi da nuna masa ƙauna, amma ya kasance a benci har aka kammala wasan da Inter Miami ta ci ƙungiyar Hong Kong 4-1 ranar 4 ga watan Fabrairu.

Dumbin mutane wajen 40,000 da suka sayi tikitin shiga kallon wasan a kan duk ɗaya dala 125 don kawai su ga Messi mai shekara 36, sun yi ihun ce a mayar musu da kudinsu, tare da yi wa Messi ihu bayan kammala wasan.

Wasu masu sharhi sun fassara rashin buga wasan da Messi ya yi a matsayin wulaƙanci ga China bayan da aka gan shi ya buga wani wasan sada zumunci na minti 30 da ƙungiyarsa ta yi da Japan kwanaki kaɗan bayan wancan wasan.

'Kyakkyawar dangataka'

A wani saƙo da aka wallafa a wata kafar sada zumunta ta China mai suna Weibo a ranar Litinin da marece, fitaccen ɗan wasan na duniya ya yi watsi da zarge-zargen, yana cewa rashin buga wasan nasa "ba dalili ne na siyasa ba."

Ya ce ai da haka ne da "ba ma zai je" Hong Kong ɗin ba gaba ɗaya.

"Kamar yadda kowa ya sani, ina son yin wasa da kuma kasancewa a kowane wasa," ya faɗa.

A bidiyon da Messi ya wallafa, ya yi magana kan cewa "akwai dangantaka mai ƙarfi kuma mai kyau" tsakaninsa da China, ƙasar da ya ce ta yi abubuwa masu yawa.

Ya ce abin da ya sa bai buga wasan ba saboda ya ji rauni ne, yana mai cewa cinyarsa ce ta kumbura.

Magoya bayansa a dandalin Weibo sun yi gaggawar mayar da martani a ƙasan bidiyon, inda wasu suka nuna goyon bayan Messi.

Wani magoyin bayansa ya rubuta cewa "Na yarda cewa ɗan wasan yana sonmu kuma ba zai taɓa yin wani abu na raini ga masoyansa ba. Yana ganin darajar duk wani magoyin bayansa.

AFP