Tun a makon jiya ne Madrid ta lashe kofin a karo na 36, yayin da ya rage wasanni huɗu a kammala gasar. Don haka ne suke dakon ranar da za a gabatar musu da kofin. / Photo: Reuters

Za a gabatar wa da zakarun Sifaniya, Real Madrid da Kofin LaLiga na 2023/24 sau biyu a mako mai zuwa, sakamakon rashin daidaito tsakanin ƙungiyar da hukumar da ke kula da gasar, wato RFEF.

Tun a makon jiya ne Madrid ta lashe kofin a karo na 36, yayin da ya rage wasanni huɗu a kammala gasar. Don haka ne suke dakon ranar da za a gabatar musu da kofin.

Sai dai ba za a yi bikin gabatarwar ba a lokacin wasan da Madrid za ta buga na gaba tare da Granada, ranar Asabar mai zuwa. Madrid da masoyanta za su jira har sai ranar Talata 14 ga Mayu, lokacin da Madrid za ta buga wasa da Alaves a filinsu na Santiago Bernabeu.

Hukumar RFEF ta yi niyyar gabatar da kofin a wasan Asabar din nan, a filin wasa na ƙungiyar Granada. Sai dai Real Madrid ta nemi a ɗage bikin saboda akwai yiwuwar a ranar ne Granada za ta faɗo daga matakin LaLiga.

Matuƙar Madrid ta doke Granada ko ƙungiyar Mallorca ta ci maki uku a wasanta da Las Palmas, to Granada za ta ƙare da makin da ba za ta iya fita daga jerin ƙungiyoyi uku na ƙarshen-ƙarshe a teburin LaLiga ba, kuma ba za ta buga gasar LaLiga a baɗi ba.

Wannan ne ya sa Madrid ta ga rashin dacewar a ce an gabatar musu da kofi suna shagali, daidai lokacin da wani kulob ɗin ke alhinin rasa matsayin buga wasa a matakin ƙwararu na ƙasar Sifaniya ba.

Sakamakon haka ne ya sa a yanzu za a gabatar da kofin ga Madrid a filin atisayensu a safiyar Lahadi. Wannan zai ba su damar nuna wa masoyansu kofin a wani biki da zai gudana a dandalin Cibeles Fountain a zauren City Hall na birnin Madrid.

Daga nan ne za a kuma yin wani bikin gabatar da kofin a filin wasan Madrid, wato Bernabeu, lokacin wasansu da Alaves ranar Talata.

TRT Afrika