Safiyanu Sule (Bature), wani masoyin Manchester United a birnin Kano na Nijeriya ya ce ba lallai ya je kallon wasan da Man U za ta buga da Man City a maraicen yau ba, saboda fargabar shan kashi a wasan nasu na gasar Firimiya.
"A matsayina na mai goyon bayan Manchester United, muna cikin fargaba duba da yadda Haaland ya dawo kan ganiyarsa, inda ya zura ƙwallaye biyar a wasansu na baya," in ji Bature.
Man City ta lallasa Luton Town da ci 6-2 a wasansu na gasar FA, inda Haaland ya ci ƙwallaye biyar rigis, ranar Talatar da ta gabata.
A maraicen yau ne Man City, wadda take mataki na biyu a teburin Frimiya da maki 59 daga wasanni 26, za ta kece raini da Man U, wadda ke mataki na 6 a tebur, da maki 44 daga wasanni 26.
Gwarzon ɗan wasa Haaland shi ne ya fi zura ƙwallaye a kakar bara a gasar Firimiya, inda a bana ma yake kan gaba a jerin maciya ƙwallo, bayan zura ƙwallaye 17 ya zuwa yanzu.
Wani dalili da ke tsorata masoya United shi ne ganin cewa farkon lokacin da Haaland ya je City, da aka masa tambaya kan wane kulob yake mararin fafatawa, sai ya ce "Ba na son ambata wa, amma Manchester United ne, tabbas!"
A wasan Haaland na farko da abokan hamayyarsu kuma makwabtansu United, ya ci ƙwallaye uku kuma ya taimaka aka ci ƙarin guda biyu, inda suka yi nasara kan United da ci 6-3 a filin wasansu na Etihad.
A wasan Man City da Man United na ƙarshe kafin yau, wanda aka buga a watan Oktoba na bara a gasar Firimiya, Haaland ya fasa ragar United da ƙwallaye biyu inda aka tashi suna da ci 3-0 a gidan United na Old Trafford.
Wani ƙarin dalili da masoya United ke tararrabin wasansu da Man City shi ne ganin cewa tawagarsu ta sake samun koma-baya a ƴan kwanakin nan, bayan farfaɗowar da suka yi na ƴan makonni.
A wasan ƙarshe da ta buga a gasar Firimiya, United ta sha kaye a hannun Fulham da ci 2-1, duk da cewa Fulham kulob ne da ke ƙasa-ƙasan teburi a mataki na 12.
Baya ga tsoron Haaland, masoya Man U suna tararrabin Kevin De Bruyne wanda a wasan City na ƙarshe ya tallafa wajen cin ƙwallaye har huɗu shi kaɗai.
A karawa sau huɗu da Man City ta yi da Man United tun bayan zuwan Haaland, City ta yi nasara sau uku, yayin da United ta yi galaba sau ɗaya tak.