Pep Guardiola

Masana harkar kwallon kafa masu bibiyar wasan kofin Firimiya na Ingila, suna jajanta halin da kulob din Manchester City yake ciki, bayan da ya ci wasa daya kacal cikin wasanni biyar na baya-bayan nan da ya buga.

Sai dai da yake sharhi kan yanayin da kulub dinsa ke ciki, mai horar da 'yan wasa Pep Guardiola ya ba da uzurin cewa ana kallon Man CIty a sikeli daban da na sauran kungoyoyin da ke buga gasar Firimiya.

A cewar Guardiola, "Abin da ake cewa ba ma yi, ba a zargin ƙawayenmu da rashin yi. Ana ta maganar wai ƙungiya ɗaya ce kawai za ta gaza cin kofin Firimiya, wato mu. Kenan sauran kungiyoyin, [cin wasa] kadai wata babbar nasara ce".

A wasan City na karshen mako, sai da aka kai ruwa rana kafin kungiyar ta yi nasara da ci biyu da daya, kan kulob din Luton Town, wanda shi ne na uku a kasan teburin Firimiya.

Hasali ma, Luton ne suka fara zura wa CIty kwallo ana dab da kammala zagayen farko na wasan da aka buga a filin wasa na Kenilworth Road da ke garin Luton. Sai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sannan City ta rama kuma ta kara kwallo guda.

Nasarar ce ta taimaki Man City daga kara ruftawa kasa, wanda ya kunshi rashin yin nasara a wasanni biyar a jere, wanda rabonta da haka, tun shekarar 2009. Shi kansa Guardiola, bai taba samun rauni makamancin haka ba a tarihinsa.

Wannan rashin taka rawar gani ta sa Man City ta kare da maki shida daga maki 15 da ya kamata ta samu cikin wasanninta biyar na karshe.

Kungiyar ta yi rashin nasara sau daya, kuma ta yi kunnen doki sau uku, kafin wannan nasarar ta ranar Lahadi.

Hakan ya janyo masu sharhi sun fara kallon kulob din da ke rike da kofin Firimiya na bara, a matsayin wanda ke fama da wasu matsalolin da suka dakushe tagomashinsa, tun bayan cin kofuna uku a kakar bara.

Ko zargin na Guardiola kan cewa ba a yi wa kulob din nasa adalci gaskiya ne? Za a gani a wasannin da City za ta buga nan gaba.

Kulob din dai yana neman kafa tarihi na cin kofin Firimiya sama da sau uku a jere, wanda ba wanda ya taba yin hakan a baya.

A yanzu dai akwai tazarar maki hudu tsakanin City da Liverpool, wadda ke jan ragamar teburin na gasar Firimiya.

TRT Afrika