Yayin da aka rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ta Janairun, wani abu da ya ja hankali masoya ƙwallo musammam masu bibiyar gasar Firimiya ta Ingila, ita ce ƙaurar da Marcus Rashford ya yi daga Mancheter United zuwa Aston Villa a matsayin ɗan wasa na aro.
Kasuwar cinikin ta hunturun 2025 ta rufe ne ranar Litinin 3 ga Fabrairu, maimakon 31 ga Janairu.
Ƙungiyoyi da dama sun samu sayo 'yan wasa manya da ƙanana don inganta tawagarsu, yayin da wasu suka samu kuɗi ta hanyar sayarwa ko ba da aron 'yan wasa.
Shahararren ɗan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya yi hannun-riga da ƙungiyar bayan samun saɓani da sabon koci Ruben Amorim.
Sai dai tafiyar ɗan wasan zuwan Aston Villa ba ta zo yadda aka so ba, saboda Villa za ta ɗauke kashi 75 ne na albashin Rashford, kuma babu tabbacin sayen ɗan wasan a kwantiragi.
Kwantiragin ta ƙunshi zaɓin sayensa ne kan farashin da bai taka kara ya karya ba, wato fam miliyan 40, duk da a zahiri farashin Rashford a kasuwa a bazarar 2023 ya ninka wannan adadi sau uku.
Wani abun da ba shi aka so ba shi ne, yadda Manchester United ta amince da sakin Rashford zuwa wata ƙungiya da ke Ingila kuma take kishiyarta a gasar Firimiya, maimakon wata ƙungiyar ƙasar waje.
Wannan na nufin ɗan wasan ba zai samu damar huce haushi kan tsohuwar ƙungiyarsa ba, domin ba zai buga wasan hamayya da su ba, balle ya iya cin su ƙwallo.
Damarmaki a Villa
A zahiri yake cewa Villa ba nan ne zaɓin da Rashford ya so samu ba, saboda ya yi burin tafiya manyan ƙungiyoyin Turai kamar Barcelona, kafin rashin kuɗin ya hana ƙungiyar ɗaukarsa.
Aston Villa dai na buƙatar ƙara ƙarfin tawagarta a gaba bayan ɗan wasansu Jhon Duran ya zaɓi komawa taka leda a Saudiyya, kuma Rashford zai iya ba mara-ɗa-kunya.
Duk da akwai masu ganin Villa ta maye gurbin ɗan wasa mara kishi, da wani mara kishin, amma dai Rashford zai yi ƙoƙarin ba wa tsohon kocinsa na Man U Ruben Amorim kunya, saboda korar karen da ya masa.
Sannan akwai yiwuwar cewa kocin Aston Villa, Unai Emery wanda ya yi suna wajen inganta tasirin 'yan wasansa, zai taimaki fito da kaifin tagomashin Rashford wanda tauraruwarsa ta yi duhu a baya.
Ko ma dai me zai faru tsakanin Villa da Rashford, ƙungiyar na da damar mayar da shi da United a ƙarshen kakar bana, idan ya gaza yin abin-a-zo-a-gani.
Rashford ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa, komawarsa Villa ta zo masa da sauƙi saboda bai bar Ingila ba, koma ba sai ya koyi wani yare ba, kuma ya san yawancin 'yan sabuwar ƙungiyar tasa.
Kuma zai samu damar buga gasar Zakarun Turai, kuma akwai yiwuwar zai samu damar buga gasar a baɗi, saɓanin idan da ya zauna a Manchester United.