Kylian Mbappe, ɗan wasan gaba na PSG ta Faransa ya aika saƙon gargaɗi ga ƙungiyar Barcelona, gabanin wasansu na zagayen kwata-fainal a gasar Zakarun Turai.
Tarihi ya nuna Mbappe ya taɓa cin Barcelona ƙwallaye uku a wasa guda a gasar ta Zakarun Turai, a shekarar 2021 inda PSG ta doke Barcelona da ci 4-1 a haɗuwar farko ta wasansu da aka buga a birnin Paris.
Da yake magana da jaridar Telefoot, Mbappe ya ce, "Na shirya, kuma kamar kullum ba zan ɓuya ba. Ganin yadda muke da tawaga mai ƙarfi, na tabbata za mu yi iya ƙoƙarinmu, sannan sakamakon... a hannun Allah yake."
Haka kuma Mbappe ya yi magana kan PSG a kakar bana, inda ya ce, "Kamar a bara, mun shiga mafi muhimmancin lokaci na kakar bana. A ƙarshen Afrilu za mu gane gwargwadon kyawun kakar ta bana."
Ana zargin akwai saɓani tsakanin manajan PSG Luis Enrique da Mbappe tun watannin baya, wanda ake ganin shi ya sa ɗan wasan ya ƙi tabbatar da cigaba da kasancewarsa a ƙungiyar, kuma an yi ta barinsa a benci ko a sauya shi yayin wasa.
Rahotannin sun nuna cewa Mbappe zai tafi real Madrid a kakar baɗi, kuma ana sa ran zai zage dantse don nuna wa Real Madrid ƙarfinsa a wasan PSG da Barcelona ranar Laraba, 10 ga Afrilu.