Babban kocin ƙungiyar Lazio ta Italiya, Maurizio Sarri ya ajiye aikinsa na horar da ƙungiyar, bayan jerin rashin nasara a wasannin da ƙungiyar ta buga a baya-bayan nan a gasar Serie A ta Italiya.
Yayin da kamfanin dillancin labarai na AFP ta tuntuɓi ƙungiyar, Lazio ta ƙi ta tabbatar da labarin ko ta ƙaryata cewa Sarri ya ajiye aiki.
Lazio na mataki na tara a teburin gasar Serie A, kuma alamu suna nuna zai yi wa kulob ɗin wahala ya samu shiga jerin ƙungiyoyi biyar na saman tebur, don ya iya buga ɗaya cikin gasannin nahiyar Turai a baɗi.
Duk da cewa a bara Lazio ta kammala gasar a mataki na biyu, a kakar bana sun yi rashin nasara a wasanni 12 cikin 28 da suka buga zuwa yanzu.
A ranar Litinin ne ƙungiyar Udenese da ke mataki na 13 a teburin ta doke Lazio da ci 2-1, a gidan na Lazio. Wannan rashin nasara ita ce ta huɗu cikin wasanni biyar da Lazio ta buga a gasar Serie A.
Fita daga gasar Zakarun Turai
A makon farko na Maris ɗin nan ne Bayern Munich ta yi waje da Lazio a gasar Zakarun Turai, bayan ta lallasa ta da ci 3-0 a wasanni karo biyu, duk da cewa a wasan farko Lazio ce ta ci 1-0.
Fitar da Lazio a matakin 'yan 16 na Zakarun Turai ya dagula wa koci Sarri lamari.
Amma har yanzu Lazio tana da sauran fata, kasancewa sun kai matakin dab da na ƙarshe a gasar Kofin Italiya, inda za su kara da Juventus a wasanni biyu.
A shekarar 2021 ne Sarri ya karɓi ragamar horar da Lazio bayan ya ɗauki shekara guda ba ya horar da kowace ƙungiya, tun bayan da ya jagoranci Juventus wajen cin kofin Serie A a tsakiyar annobar Covid-19.
Shekarar Maurizio Sarri 65 a duniya, kuma shi ne ya ci gasar Europa League a shekarar 2019 tare da Chelsea.