A shekarar 2022 ne Erik ten Hag ya zo Manchester United daga ƙungiyar Ajax. / Hoto: Reuters

Bayan tsawon lokaci ana tababar makomar kocin Manchester United, Erik ten Hag, a yanzu dai hukomomin ƙungiyar sun daidata da shi inda suka tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2026.

Kocin wanda ɗan asalin Holland ne ya ayyana cewa yanzu an samu 'cikakken haɗin-kai' tare da kamfanin da ke jagorantar ƙungiyar, INEOS mallakin babban ɗan kasuwa Sir Jim Radcliffe.

Ten Hag ya ce, “Ina matuƙar farin cikin cim ma yarjejeniya da kulob ɗin don ci gaba da aiki tare. Idan muka duba shekaru biyu na baya, muna alfahari da lashe kofuna biyu da wasu nasarori idan an kwatanta daga inda muke lokacin da na shigo".

Sai dai an ambato shugabannin kamfanin da ke da rinjayen hannun-jari a ƙungiyar suna gargaɗin cewa 'akwai aiki a gaba', yayin da Ten Hag ke shirin ci gaba da jagorantar Man United.

Wannan mataki ya nuna cewa Man United ta kawo ƙarshen neman sabon kocin da za ta maye gurbin Ten Hag da shi. Kuma ya nuna cewa sun cim ma matsaya kan dacewarsa na cigaba da jagorantar kulob ɗin.

United ta yi amfani da saɗarar cikin kwantiragin da ta ba da damar tsawaita asalin kwantiragin shekara uku da Ten Hag ya sanya wa hannu, wanda hakan ke nufin ƙa'idojin sabuwar kwantiragin daidai suke da na baya, kuma Ten Hag ba zai samu ƙarin albashi ba.

Masu sharhi kan wasanni suna kallon wannan mataki na United a matsayin sakayya gareshi saboda lashe kofin gasar FA da ya yi, inda ya doke Manchester City.

Bayan sanarwar tsawaita kwantiragin, rahotanni sun nuna cewa kulob ɗin na shirya ɗauko sabbin jami'an horar da 'yan wasa, ciki har da tsohon ɗan wasanta Ruud van Nistelrooy, don shirya wa kakar bana da za a fara nan da wasu makonni.

TRT Afrika