Manchester City za ta kara da Sevilla a gasar cin kofin UEFA karo na 48

Manchester City za ta kara da Sevilla a gasar cin kofin UEFA Super Cup karo na 48 a ranar Laraba.

Kungiyar, wadda ta lashe gasar Zakarun Turai ta 2023, za ta kara da Los Palanganas, zakarun UEFA Europa League na 2023, a filin wasa na Georgios Karaiskakis da ke Piraeus a kasar Girka.

Man City za ta buga wasanta na farko a gasar cin kofin ‘Super Cup’ na karshe, yayin da Sevilla wacce ta yi rashin nasara a gasar har sau biyar, za ta fafata a bana don lashe kofinta na biyu.

Kungiyoyin La Liga na kasar Sifaniya da Real Madrid da Barcelona da kuma AC Milan na Seriya A na Italiya, sun kafa tarihi wa kungiyar wajen samun nasara mafi yawa, inda kowacce daga cikinsu ta yi nasara lashe gasa har sau biyar.

Barcelona ta yi rashin nasara a gasar cin kofin Super Cup sau hudu sai Real Madrid sau uku da kuma AC Milan sau biyu.

Kungiyoyin Sifaniya sun lashe gasar cin kofin ‘Super Cup’ sau 10 cikin 14 da aka taba bugawa.

Real Madrid ta lashe kofuna hudu a shekarar 2014 da 2016 da 2017 da kuma 2022, yayin da Barcelona ita ma ta lashe kofuna uku a 2009 da 2011 da kuma 2015 sai Atletico Madrid uku, a 2010 da 2012 da kuma 2018.

Galatasaray ta lashe kofin UEFA Super Cup a shekara ta 2000, inda ta zama Kungiya daya tilo kuma ta farko daga Turkiyya da ta taba lashe kofin.

Gasar ta cin kofin UEFA Super Cup wasa ne da ake bugawa duk shekara tsakanin kugiyoyin da suka yi nasarar lashe gasar UEFA Champions da UEFA Europa a wasan bara.

AA