Manchester United na dab da ficewa daga Gasar Zakarun Turai bayan FC Copenhagen ta doke ta da ci 4-3 a fafatawar da suka yi ranar Laraba a babban birnin Denmark.
Kungiyar ta soma wasan da kafar-dama yayin da Rasmus Hojlund ya zura kwallo biyu a ragar tsohuwar kungiyarsa a kasa da awa daya.
Sai dai jan katin da aka bai wa Marcus Rashford ya dagula wa United lissafi inda ta sha kashi sau uku cikin wasanni hudu da ta yi a Rukunin A.
Mohamed Elyounoussi da Diogo Goncalves ne suka farke wa Copenhagen kwallaye biyu da aka zura mata kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Daga bisani Bruno Fernandes ya sake mayar da United a gaba bayan ya ci kwallo daya, amma kwallaye biyu da Lukas Lerager da Roony Bardghji suka ci wa Copenhagen ya ba su damar yin nasara a wasan Gasar Zakarun Turai karon farko tun 2016.
Wannan wasa ya sa United ta zama ta karshe a Rukunin A, inda take da maki uku wato tana bayan Galatasaray da Copenhagen masu maki hudu-hudu, yayin da take da sauran wasanni biyu.
Red Devils za su tafi Galatasaray nan da mako uku sannan daga bisani su karbi bakuncin Bayern Munich.