Mahukuntan Manchester United sun tabbatar da naɗa Ruben Amorim, ɗan asalin Portugal a matsayin sabon koci ƙungiyar, kwanaki kaɗan bayan sallamar Erik ten Hag.
Sai dai sabon kocin ba zai karɓi aikin zama babban kocin tawagar ta United ba, har sai nan da kusan makonni biyu, inda ƙungiyar ta ce Ruud van Nistelrooy zai ci gaba da riƙe ƙungiyar a halin yanzu.
Da ma an yi ta raɗe-raɗin cewa ƙungiyar tana tattaunawa da Amorim, wanda a yanzu zai bar ƙungiyarsa ta Sporting CP ranar 11 ga Nuwamba.
Sanarwar da Man United ta fitar ta ce, "Manchester United tana farin cikin sanar da naɗa Rúben Amorim a matsayin Babban Koci na babbar tawagar maza."
Kwantiragin shekara 3
Amorim ya sanya hannu kan kwantiragi har zuwa Yunin 2027, tare da ƙarin shekara guda. Amma ba zai karɓi aiki ba sai ranar Litinin 11 ga Nuwamba bayan ya cika ƙa'idojin biza, da sharuɗɗan barin ƙungiyarsa ta Sporting CP.
Amorim dai yana cikin manyan koci a Turai kuma ya cim ma nasarori sanda yana buga ƙwallo, da kuma a aikinsa na horar da 'yan wasa.
Ya lashe gasar Primeira Liga ta Portugal sau biyu tare da Sporting CP, wanda ba su taɓa yin hakan ba tun shekara 19 da suka wuce.
Shekarun Amorim 39 kuma zai shiga rukunin matasan koci a gasar Firimiya. United za ta biya Fam miliyan £9.2 (dala miliyan $11.8) a matsayin diyya ga Sporting.
A yanzu dai Manchester United tana mataki na 14 a gasar Firimiya bayan wasanni 9, inda suka kori tsohon koci Erik ten Hag, suka nada Van Nistelrooy a matsayin riƙo.
Nistelrooy ya jagoranci United wajen lashe wasansu na ƙarshe a gasar Carabao Cup, inda suka doke Leicester City da ci 5-2.