Manchester United ta Ingila ta sanar da soke liyafar cin abinci da ba da kyaututtuka ta ƙarshen kaka, wanda ƙungiyar ta saba gabatarwa lokacin kammala kakar wasa ta gasar Firimiya.
United ta sanar da hakan ne saboda tana son 'yan wasanta su mayar da hankali kan wasan ƙarshe na gasar FA wanda za a buga ranar 25 ga watan nan na Mayu.
Wannan labari bai ba da mamaki ba, sakamakon cewa United na gab da ƙare kakar wasa mara armashi, inda abin da ya rage mata kawai shi ne fatan cimma nasarar lashe kofin gasar FA na bana.
Sai dai abin zai iya yi wa Man U wahala, saboda abokiyar karawarta Manchester City ce, wadda ko a bara ma ita ta doke ta wajen lashe kofin na gasar FA, baya ga cewa Man City ɗin ce ta lashe gasar Firimiya a karo na 3 a jere a baran.
A da, an shirya gudanar da liyafar cin abincin da ba da kyaututtuka ne ranar 20 ga Mayu, a cewar shafin The Athletic. Sai dai bayan tattaunawa da kocin ƙungiyar wanda ke cikin matsi, Erik ten Hag, an soke bikin.
Liyafar ta saba samun halartar duka 'yan wasan Man United, tawagar maza da ta mata, da ma tawagogin makarantar horar da 'yan wasa. A wajen bikin ne ake bayar da kyautar "Sir Matt Busby" da ake bai wa gwarazan matasan 'yan wasa na ƙungiyar.
An taɓa soke irin wannan biki a kakar wasa ta 2021/22, lokacin da United ta yi fama ƙarƙashin jagorancin tsohon koci Ralf Rangnick, wanda da ƙyar United ta ƙare a matsaki na shida a gasar Firimiya.
A yanzu dai ana kallon kocin ƙungiyar na yanzu, Erik ten Hag yana cikin haɗarin kora daga muƙaminsa, musamman idan ya gaza kai United ga nasara a wasan ƙarshe na gasar FA da za a buga nan da mako biyu.
Baya ga ƙoƙarin doke Man City don lashe kofin FA, United tana da 'yar damar cimma nasarar haye wa gaban Newcastle da Chelsea a teburin Firimiya, inda za ta samu gurbin buga wasa a gasannin Turai, duk da dai ba a babbar gasa ta Zakarun Turai ba.