Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya yi bayani kan makomar matashin ɗan wasa, ɗan asalin Turkiyya, Arda Guler, yayin da ake raɗe-raɗi cewa zai bar ƙungiyar.
Ancelotti ya yanke hukuncin cewa Arda Guler, wanda tauraruwarsa ke haskawa, zai ci gaba da kasancewa a kulob ɗin a kaka mai zuwa, duk da rahotannin da ke cewa zai tafi AC Milan ta Italiya.
Madrid ta ɗauki ɗan wasan ne daga ƙungiyar Fenerbahce ta Turkiyya a bazarar bara kan kuɗin da aka ce ya kai Fam miliyan £25.4 (dala miliyan $32). Amma ba a faye ganin ɗan wasan ɗan shekara 19 a filin wasa ba.

Sai dai bayan ya ci ƙwallo a karon farko na wasan da aka fara da shi, ranar Juma'a inda Real Madrid ta doke Real Sociedad, wanda aka tashi da ci 1-0, manaja Ancelotti ya ce ɗan wasan gaban babu inda zai tafi.
Ancelotti ya faɗa wa manema labarai cewa, "Babu shakka shi [Guler] zai zauna a nan har baɗi. Ina ga tawagarmu ta yi ƙoƙari sosai. Ya yi ƙoƙari, ya yi yaƙi. Zai zauna a nan shekara mai zuwa, ba ni da shakka kan haka".
"Shi matashi ne sosai. A hankali a hankali zai taka rawarsa. A bayyane yake ya ci ƙwallaye sama da mintunan da ya samu buga wasa. Wannan ita ce baiwar da yake da ita," in ji Ancelotti.

Ana yi wa Guler laƙabi da 'Messin Turkiyya', amma wasanni takwas kacal ya buga wa Madrid cikin duka gasanni a kakar bana, wanda haka ne ya janyo ake jita-jitar zai tafi Milan, ko Borussia Dortmund ko Bayer Leverkusen.
Sai dai ɗan wasan wanda kwantiraginsa za ta ƙare a 2029, zai so ya ci gaba da zama a Madrid.
Shafin Goal ya ruwaito cewa Guler ya gaya wa shafin Madrid ranar Juma'a cewa, "Wannan shi ne kulob mafi kyau a duniya, kuma cin ƙwallo yana cikin mafi daɗi a wajena. Ina alfahari da zamana a nan da kuma cewa na ci ƙwallo. Ina yi wa kowa godiya."

Bayan taimakawa Real Madrid ƙara kai wa kusa da ɗaga kofin LaLiga na bana a wasansu da Real Sociedad, Guler zai yi fatan samun gurbin buga sauran wasanni biyar da suka rage a gasar LaLiga.