A wasansa na farko bayan an dakatar da shi kan ziyarar da ya kai Saudiyya ba tare da izini ba, wasu magoya bayan Paris St-Germain sun yi wa Lionel Messi ihu yayin da kungiyarsa ta doke Ajaccio da ci 5-0.
Ya yi wasansa na farko ne duk da cewa wa'adin mako biyun da aka dakatar da shi bai cika ba, lamarin da ya sa wasu ke ganin an yi sulhu ne tsakanin kungiyar da dan wasan.
A wasan da aka yi ranar Juma’a, kungiyoyin biyu sun tashi da ‘yan wasa goma-goma bayan Thomas Mangani ya kai wa Achraf Hakimi naushi shi kuma ya rama.
Harin da ‘yan wasan suka kai wa juna ya sa alkalin wasa ya kore su daga filin wasa ta hanyar nuna musu jan kati.
Fabian Ruiz da Hakimi ne suka fara zura wa PSG kwallaye a ragar Ajaccio kafin hutun rabin lokaci.
Mbappe ya zura kwallaye biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kafin Mohamed Youssouf, dan kungiyar Ajaccio, ya zura kwallo a ragar kungiyarsa, lamarin da ya sa Ajaccio ta koma gasa ta kasa da Lig1.
Minti 67 da fara wasa ne damar Ajaccio ta zura kwallo a ragar PSG ta zo, sai dai kuma kwallon da Mickael Barreto ya bugo ta haura saman ragar PSG ne.
Messi dai ya buga wasa na minti 90 a wasansa na farko bayan PSG ta dakatar da shi kan tafiyar da ya yi Saudiyya ba tare da izini ba.
PSG tana neman maki hudu don ta tabbatar da lashe kofin gasar Lig1 na Faransa a karo na 11.
PSG ta fi Lens da ke biye da ita da maki shida, kuma tana da wasanni uku da za ta buga kafin a karasa gasar.