A wasanta na mako na bakwai a gasar Firimiya, Liverpool ta doke Crystal Palace da ci ɗaya mai ban-haushi, inda ta buɗe sabuwar tazarar maki huɗu a kan teburin Firmiya.
Liverpool na gaban Manchester City da maki huɗu kuma za ta ci gaba da jan ragamar teburin, duk da ratarta za ta iya raguwa idan City ta samu maki ɗaya ko uku a wasanta da Fulham a maraicen yau.
Ɗan wasan Liverpool na gaba Diogo Jota ne ya ciyo mata ƙwallo guda tun a minti na tara. Sai dai a minti na 79 da wasan, sanannen mai tsaron gidanta Alisson Becker ya samu rauni, inda aka maye gurbinsa da Vitezslav Jaros.
Gabanin cire shi, Alisson, wanda ɗan asalin Brazil ne, ya yi ƙoƙari a lokuta da dama wajen kawar da bara da 'yan wasan Palace suka yi ta kawowa.
Damar farko
Nasarar ta Liverpool tana da muhimmanci saboda ba a gida ta buga wasan ba, kuma wannan ce nasara ta tara a wassan 10 da ta buga ƙarƙashin sabon koci Arne Slot.
Ita kuwa Crystal Palace ta ci gaba da rashin nasara a duka wasanni bakwai da ta buga a kakar gasar Firimiya ta bana, inda ta yi canjaras sau uku, ta kuma yi rashin nasara sai huɗu, kuma take mataki na ukun ƙarshe cikin 'yan waje-rod.