| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Fifa
Messi ya doke dan wasan Paris St Germain Kylian Mbappe da Erling Haaland na Manchester City inda ya zama gwarzon dan kwallon kafa na FIFA na shekarar 2023.
Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Fifa
Messi, mai shekara 36, ya soma 2023 a kungiyar kwallon kafar PSG amma a watan Yuli ya tafi Amurka inda yake murza leda a Inter Miami. / Hoto: Reuters / Others
16 Janairu 2024

Shahararren dan kwallon kafar Ajentina Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar duniya na Fifa na 2023.

An sanar da hakan ne a wani biki da aka gudanar a London ranar Litinin da maraice.

Messi ya doke dan wasan Paris St Germain Kylian Mbappe da Erling Haaland na Manchester City.

Golan Man City, Ederson, ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron raga na shekarar 2023 bayan ya fafata da golan Real Madrid Thibaut Courtois da golna Al Hilal, Yassine Bounou.

Messi, mai shekara 36, ya soma 2023 a kungiyar kwallon kafar PSG amma a watan Yuli ya tafi Amurka inda yake murza leda a Inter Miami.

Wannan ne karo na uku da ya lashe kyautar - a 2019 da 2022 da kuma 2023.

MAJIYA:TRT Afrika