Messi ya ci sauran kyautukan Ballon d'Or  ne yayin da yake murza leda a Barcelona  / Hoto: AFP

Shahararren dan kwallon kafar duniya Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'Or karo na takwas a bikin da aka yi a a Paris ranar Litinin.

Dan kasar Ajentina ya cika burinsa na rayuwa lokacin da ya jagoranci tawagar kasarsa wajen lashe Gasar cin Kofin Duniya da aka gudanar a Qatar a 2022 bayan ya kwashe shekaru ba su ci kofin ba.

'Yar kasar Sifaniya Aitana Bonmati ce ta lashe kyautar Ballon d'Or rukunin mata bayan ta jagoranci kasarta wajen cin Kofin Gasar Kwallon Kafar Mata ta Duniya da aka yi a watan Agustan da ya gabata.

Lionel Messi, wanda yanzu yake murza leda a Inter Miami da ke Amurka, ya shahara ne a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona inda a can ne ya lashe dukka kyautar Ballon d'Or na baya. Sai dai ya raba gari da kungiyar cikin yanayi mai ban tausayi.

Daga Barcelona dan wasan na Ajentina ya koma Paris Saint-Germain, wacce ya bari a karshen kakar bara.

Messi ya doke fitaccen dan wasan gaban Manchester City Erling Haaland wanda aka sa rai zai lashe kyautar saboda bajntar da ya nuna a kungiyar.

Haaland ya jagoranci City wajen lashe gasa uku a kakar wasa daya – Gasar Firimiya, Gasar Zakarun Turai da kuma Gasar cin Kofin FA – inda ya ci kwallo 52.

TRT Afrika da abokan hulda