Aymeric Laporte ya kwashe   shekara biyar da rabi a City./Hoto: Reuters

Dan wasan tsakiyar Sifaniya Aymeric Laporte zai tafi Saudiyya don taka leda tare da Cristiano Ronaldo da Sadio Mane, bayan rasa matsayinsa a kungiyar Manchester City.

Laporte, mai shekara 29, zai tafi kungiyar Al Nassr, kamar yadda Manchester City ta sanar a ranar Alhamis din nan kan dala miliyan 30.

Ya sauka daga jerin sunayen ‘yan wasa masu tsaron gida na Manchester City, bayan an sanya hannu da Josko Gvardiol da Nathan Ake wadanda duk bahagwaye ne masu tsaron gida a Gasar Premier ta Ingila.

Tare da Ronaldo da Mane, Al Nassr ta sayi Alex Telles da Marcelo Brozovic a matsayin 'yan wasanta.

Kungiya Al Nassr na daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa hudu na Saudiyya da suka zaman a kasa karkashin Asusun ZUba Jari, wadda yake da kadarori na dala biliyan 700, kuma yake daukar nauyin harkokin kwallon kafar kasar.

A wani sakon bidiyo da Laporte ya fitar ya bayyana cewa zai bar City, shekara biyar da rabi bayan kungiyar ta saye shi daga Atletico Bilbao. Ya lashe kambi 13 a City.

Ya ce “A lokacin da na fara zuwa kungiyar, na zaku na fara lashe kambi da kofuna,” amma ya kara da cewa “Ba zan iya hasashen nasarar da za mu samu tare ba.”