Gwarzon ɗan wasan Real Madrid, ɗan asalin Faransa, Kylian Mbappe ya sayi kulob na ƙashin-kansa mai suna Cean, wanda ke aji na biyu na gasar Ligue 2 a Faransa.
Rahotanni sun ce Mbappe ya sayi mafi rinjayen hannun jarin kulob ɗin, inda zai lale zunzurutun kuɗi euro miliyan 20 (dala miliyan 22), yayin da Pierre-Antin Capton zai riƙe ragowar hannun jarin ƙungiyar ta Cean, da ya kai euro miliyan biyar.
Shekarun Kylian Mbappe 25, kuma sayen kulob ɗin ya sa ya shiga sahun mafi ƙarancin shekaru da suka mallaki ƙungiyar ƙwallo a Turai.
A sabon kulob ɗinsa na Real Madrid, Mbappe ya zamo wanda ya fi kowa ɗaukar albashi, inda aka ruwaito yana karɓar euro miliyan €15 (dala miliyan $16).
Sai dai sabon albashin nasa bai kai yadda yake karɓa a tsohon kulob ɗinsa na Paris Saint-Germain ba, amma akwai ƙarin kuɗin da zai samu daga sa hannu a kwantiraginsa, wanda ya kai euro miliyan €100 (dala miliyan $108).
A farkon 2024, mujallar Forbes ta ayyana yawan kuɗin da Mbappe yake samu daga kwangilolin talla, wanda ya kai dala miliyan $20, wanda kuma ya sanya shi cikin rukunin masu arziƙi a duniya.
A baya da yana ƙarami, Mbappe ya kusa shiga ƙungiyar ta Caen, amma sai batun ya rushe bayan da kulob ɗin ya faɗo daga ajin ƙwararru na Ligue 1.
Akwai yiwuwar Mbappe wata rana ya buga wa kulob ɗin nasa, irin yadda Didier Drogba ya yi a kulob ɗin Phoenix Rising na Amurka, a 2017.