Hukumar Kwallon Kafar Afirka (CAF) ta fitar da jerin sunayen 'yan wasa da za su yi takarar lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar Afirka wato CAF Awards 2023.
Za a gudanar da bikin bayar da kyautar ne ranar 11 ga watan Disamba a birnin Marrakech na kasar Maroko.
A cewar dokokin CAF, masu ruwa da tsaki a fagen kwallon kafa sun tattara sunayen masu yin takara na rukuni daban-daban ne daga watan Nuwamba na 2022 zuwa watan Satumba na 2023.
'Yan wasa 30 ne ke takarar gwarzon dan kwallo kafa, yayin da 'yan wasa 20 ke takarar gwarzon kwallon kafa na CAF a bangaren kulob-kulob.
Kazalika mutum 10 ne suke takarar gwarzon kocin Afirka, da gwarzuwar tawagar kwallon kafa na shekara.
A karon farko, CAF ta fitar da sunayen masu takarar zama gwarzon gola na shekara (A rukunin maza da mata).
Masu ruwa da tsaki a fagen kwallon kafa wadanda suka hada da Kwararru a CAF da 'yan jarida da koci-koci da kyafin-kyaftin ne za su kada kuri'ar zaben gwarazan kwallon kafar na CAF.
CAF ta ce nan gaba za ta fitar da jadawalin gasar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta Afirka.
Latsa nan don karanta cikakken jadawalin.