Kungiyoyin kwallon kafar Saudiyya sun kashe dala miliyan 957 a kasuwar musayar 'yan kwallo.
Kudin da suka kashe bayan cire haraji a musayar ya kai dala miliyan 907, abin da ke nufi su ne na biyu wajen kashe kudi kan sayen 'yan kwallo bayan kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila, a cewar kamfanin Deloitte.
Fitattun 'yan wasa irin su Neymar da Karim Benzema na cikin 'yan wasa 94 da kungiyoyin kasar suka saya, wadanda suka hada da 'yan wasa 37 daga kungiyoyi biyar mafi daraja a Turai, in ji kamfanin da ke sanya ido kan harkokin kudi na fannin wasanni Sports Business Group.
Kungiyoyin da ke buga gasar lig na Saudiyya sun sayi akasarin 'yan kwallonsu ne daga kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila, wadanda suka samu $698m daga kasashen waje ciki har da $312m daga kungiyoyin Saudiyya.
Jumullar kudaden da aka kashe idan aka cire kudaden 'yan wasan da suka sayar, ya kai dala miliyan 907, wanda ya yi kasa da wanda Firimiya Lig ta kashe na dala biliyan 1.39.
Kungiyoyin Saudiyya sun kashe dala miliyan 148 a kungiyoyin Faransa na Ligue 1, da dala miliyan 122 a Serie A na Italiya, dala miliyan a La Ligar Sifaniya da dala miliyan 32 a Bundesligar Jamus, in ji Deloitte.
Pro Lig na Saudiyya ya hada da tawaga hudu mallakin Asusun Zuba Jari daga Kudin mai na gwamnatin kasar, sun yi ta sayen 'yan wasa don farfado da kungiyar a wani kokari na fadada hanyoyin tattalin arzikin kasar.
Alkaluman na Deloitte ba su hada da na kungiyar Al-Nassr da ta sayi shahararren dan wasan nan na Portugal ba, wato Cristiano Ronaldo, wanda ya je Saudiya a watan Janairu. Ronaldo ya zo ne karkashin kwantiragin shekara biyu da rabi kan kudin da ya kai Euro miliyan 400.
Izzy Wray daga kamfanin Sports Business Group ya ce wannan ne karo na farko tun shekarar 2016 da gasar wata kasa ta shige gaban manyan gasannin kasashe biyar na turai, wajen kashe kudi a kasuwar sayan 'yan wasa.
Wray ya ce, "Yawan adadin 'yan wasan da aka siyo da kuma kimar wadanda suka shigo gasar ta Saudiyya, ya nuna yaddar kasar ke da burin mayar da gasar ta Saudiyya ta zamo babbar gasar kwallon gafa a duniya".
"A yanzu dai ana lokacin da za a iya cewa zangon farko ne na shirin inganta gasar ta Saudiyya, kuma babban fatan daukaka ta a nan gaba, duk da karancin gwargwadon shekarun 'yan wasan da ke buga wasa a gasar a kakar bara."
Jami'an Saudiyya sun saka burin mayar da gasar da a baya ba a san da ita ba, ta zamo babbar gasa a duniya, kuma daya daga cikin manyan gasannin duniyar kwallon kafa ta duniya, ta la'akari da gogewar 'yan wasa, da yawan masu zuwa kallo, da kuma kasuwanci.