A makon da ya gabata ne Musulmai suka soma azumin watan Ramadana Photo/AA

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shirya buda baki na musamman kuma irinsa na farko a filin wasa na Stamford Bridge da ke Ingila.

Daruruwan mutane ne suka halarci buda bakin a ranar Lahadi.

Chelsea Foundation ce ta shirya buda bakin, wadda gidauniya ce ta musamman ta kulob din da ke ayyukan taimako da kuma, da kuma hadin gwiwar kungiyar Ramadan Tent Project.

Kungiyar Ramadan Tent Project ita ma na ayyuka ne na tallafi da kuma yada sakonnin Musulmai a watan Ramadana mai alfarma.

Shugaban Gidauniyar Chelsea Foundation Simon Taylor da shugaban kungiyar Islamic Relief reshen Birtaniya Tufail Hussaim da kuma dan kwallo na farko da zai buga wa Chelsea Paul Canoville na daga cikin wadanda suka halarci taron.

A lokacin da yake karin bayani ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Omar Salha, wanda shi ne ya assasa shirin na Ramadan Tent Project, ya ce suna so su hada kan jama’a ne.

Ya bayyana wannan taron a matsayin wani abu na “tarihi.”

“Kwallon kafa na hada kan mutane, amma shi ma Ramadan yana hada kan jama’a, buda baki da aka yi a fili ya mayar da wadanda ba su san juna ba abokai,” kamar yadda ya bayyana.

"Ya kara da cewa a irin wannan taron, mutane da ke da shekaru daban-daban da addinai mabambanta na haduwa."

Haka kuma shirin na Project Tent din ya sake hada wani buda bakin a gidan tarihi na Victoria and Albert da ke Landan a ranar Juma’a, inda sama da mutum 400 suka halarta.

Wadanda suka shirya buda bakin sun gode wa wadanda suka halarta.

A makon da ya gabata ne Musulmai a fadin duniya suka soma azumin watan Ramadana, inda suke azumi tun daga asubahi har faduwar rana.

AA