Kocin Manchester City, Erik ten Hag ya dage kan cewa maƙwabtansu kuma manyan abokan hamayyarsu, Manchester City ba su fi su aji ba, duk da shan kashin da suka yi a wasansu na Lahadi da ci 3-1.
Erik Ten Hag ya yi wannan ikirari ne bayan da aka yi masa tambaya kan ko galabar da aka yi a kansu ta nuna cewa akwai wagegen bambanci na kwarewa tsakanin kungiyoyin biyu da ke birnin Manchester.
A kokarinsa na nuna rashin nasarar tawagarsa ba ya nufin Man City ta kere musu a aji, Ten Hag ya yi nuni kan 'yan wasansa da ke jinya, wadanda ba su samu damar buga wasan ba.
Ya kuma ayyana galabar da aka yi kansu a matsayin wata 'yar tazara, duk da cewa Man CIty ta nuna matukar rinjaye a kusan kowane bangare na wasan, tun lokacin da Marcus Rashford ya fara ciyo musu kwallo a farkon wasan.
A wasan dai, City ta kere su kusan a duka ma'aunin kwarewa, inda United ta rike kwallo da kaso na 27 kacal cikin 100 inda City take da kaso 73.
A yawan bugun kan raga United na da 1 CIty na da 8, a kwakkwaran bugu kuma, United na da 3 City na da 27.
A yawan taba kwallo ma, United na da 478, yayin da City ke da 981. Sai a fannin ba da kwallo United na da 305 inda City ke da fasin 801. Haka ma a yawan bugun kwana United ta buga 15, inda City ta buga 2 kacal.
Da yake ba da amsa kan kokarin 'yan wasansa, Ten Hag ya ce, "Za mu iya nuna bajinta, kuma mun nuna hakan a wasan karshe na gasar FA, amma dai ranar nan ta City ce, kar ku manta da wannan. Su ne kulob din da suka fi kowa a duniya a yanzu."
Sakamakon wasan nasu ya bar Man United a mataki na 6, yayin da CIty ke gaba da su da ratar maki 18, a mataki na 2 a teburin na FIrimiya. Dukkaninsu dai wasanni 11 ne suka rage musu kafin kammala gasar.