Guardiola ya ciyo wa Manchester City jimillar kofuna 16 zuwa yanzu. / Hoto: Reuters

Yayin da Manchester City ke shirin furkantar Brighton a Gasar Firimiya gobe Asabar 9 ga Nuwamba, masu nazarin tamola za su zura idon don ganin yadda kungiyar za ta nemi fitowa daga gararin da ta shiga a 'yan kwanakin nan.

A duka wasanni uku na karshe da Man City ta buga ta sha kashi, sannan an zura mata jimillar kwallaye takwas, inda a wasanta da Tottenham aka doke ta da ci 2-1, da Bournmouth aka mata ci 2-1, sai kuma Sporting CP ta mata ci 4-1.

Duk da cewa Man City ta lashe jimillar kofuna 16, tare da kafa tarihin cin kofin Firimiya sau hudu a jera, a yanzu City ta shiga matsalar da alamu ke nuna zai mta wahalar farfadowa cikin sauri.

A makon jiya City ta rasa matsayinta na farko a teburin Firimiya, bayan wasan da Bournmouth ta doke ta a waje, inda hakan ya bai wa Liverpool damar darewa kan teburin da maki 25 daga wasanni 10, wato maki biyu sama da na City.

Wannan ne karo na uku da Man City ta taba rashin nasara a wasanni uku a jere tun bayan zuwan Guardiola kungiyar.

Kuma dokewar da Tottenham ta mata ya sa an yi waje da ita daga gasar Carabao ta Ingila, inda yanzu damarta ta cin kofi a bana ta ragu.

Abin tsoro

Wani abu da ya ja hankalin masoya da magautan Man City shi ne ganin yadda Sporting CP ta zazzaga mata ci hudu, inda ci daya kawai ta iya ramawa.

Dalili shi ne kocin Sporting da ya lallasa Guardiola, wato Ruben Amorim, shi ne sabon kocin da babbar 'yar adawar City a Ingila, Manchester United ta dauko, inda a mako mai zuwa zai zo Old Trafford ya kama aiki.

Wani abin tsoro kuma shi ne, duka shan kayen da City ta yi sun faru ne a wasan da ta buga a waje. Ga shi kuma wasan Asabar ma a gidan Brighton za a buga, kungiyar da take maki guda da Tottenham, kuma take saman Bournmouth da Man United.

Idan City ta bari aka kuma doke ta a wasan na gaba, to hakan zai kafa mummunan tarihi doke ta a karo na hudu a jere karkashin Guardiola. Wannan ya sa ana ganin wasan tamkar na a mutu ko a yi rai ga hazikin kocin.

Baya ga hadarin da wasan yake da shi kan matsayin Guardiola, wasan zai iya saka shakko kan karfin City na kare kambunta na Firimiya, saboda Liverpool za ta iya ba ta tazarar maki 5 rigis, yayin da Arsenal da Nottingham Forest suke neman karbe mataki na biyu daga hannun City.

'Yan wasan City da dama suna fama da jinya, ciki har da Rodri, Ruben Dias, John Stones, Jack Grealish, da Oscar Bobb.

Yayin da ba a saka ran 'yan wasan za su dawo buga wasa a wasan City na gaba, sakamakon wasan zai nuna alkiblar da kungiyar ta fuskanta a lokacin da ake farkon kakar bana.

TRT Afrika