Senegal na matsayi na biyu yayin da Masar ke matsayi na biyar sai kuma Kamaru da ke matsayi na bakwai a wasannin kwallon kafa a nahiyar Afirka, in ji FIFA. Hoto: TRT Afrika

Daga Brian Okoth

Kasar Maroko na ci gaba da jagorantar Afirka a matsayin kungiyar kwallon kafa ta maza da ke kan gaba a nahiyar, a cewar sanarwar da hukumar FIFA ta fitar a ranar Alhamis.

Kasashen da suka fafata a Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2022 sun kasance a matsayi na 13 a duniya, baga ga kasar Argentina da Faransa da Brazil da Ingila da Belgium da Portugal da Netherlands da Sifaniya da Italiya da Croatia da Amurka da kuma Mexico da ke biye a wannan mataki.

Makcco tana da maki 1658.49, wajen maki 5.45 tsakaninta da Mexico wacce ke a matsayi na 12.

FIFA tana amfani ne da tsarin dabarar kididdigar maki da aka sabunta a watan Satumba 2023.

Cikin tsari mai sauki, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA tana bai wa kungiyoyi matsayi bisa jimillar makin da aka samu a fafatawar da suka yi ta tsawon wani lokaci.

Manyan kasashe biyar

Kungiyar da ta yi rawar gani wacce kuma ke matsayin gaba, tana da damar samun sakamako mai kyau a cikin 'yan kwanakin nan idan aka kwatanta da kungiyar da ke matsayin baya.

A Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta AFCON ta 2021, Senegal ce ta biyu a Afirka, sannan ta 20 a duniya da maki 1600.82.

Kamaru tana matsayi na bakwai a Afirka kuma ita ce ta 43 a duniya da maki 1466.98, / Hoto: AFP

Tunisiya wacce ke matsayi na 32 a duniya, ita ce ta uku a Afirka da maki 1516.14.

Kasar Aljeriya wacce makwabciyar Tunisiya ce ita ta biyo baya da matsayi na 33 a duniya da kuma maki 1512.9.

Masar ta yi waje da kungiyoyin kwallon kafa biyar da suka fi fice a Afirka, da maki 1511.95, wanda hakan ya ba damar zama a matsayi na 35 a duniya.

Burkina Faso ta samu matsayi a fitattun kungiyoyi 10 na Afirka

Nijeriya tana matsayi na shida a nahiyar kuma ita ce ta 40 a duniya da maki 1490.48.

Kamaru tana matsayi na bakwai a Afirka kuma ita ce ta 43 a duniya da maki 1466.98, sai kasar Mali wacce ke matsayi na 47 a duniya da maki 1449.75.

Kasar Cote d'Ivoire da ke zama mai masaukin baki a gasar AFCON na 2023 - tana matsayi na tara a Afirka, kuma ta 52 a duniya da maki 1439.17

Burkina Faso, wacce ke a matsayi na 56 a duniya, ta fitar da manyan kungiyoyin kwallon kafa goma a Afirka da maki 1410.59.

Eritriya ba ta da matsayi

Duk kasashen Afirka sun kasance a jerin sunayen da FIFA fitar in ban da Eritiriya da hukumar ta ce ta gaza wajen buga wasanni na yau da kullun.

"Babu wani matsayi da aka bai wa Eritrea saboda rashin buga aƙalla wasa daya a cikin wata 48 da suka gabata da kuma rashin buga akalla wasanni biyar da kungiyoyin kasashen da aka zaba a hukumance," a cewar sanarwar FIFA ta ranar Alhamis.

Ga cikakken jerin kasashen Afirka da FIFA ta fitar a watan Oktoba 2023 da kuma matsayinsu:

1. Maroko (matsayi na13 a duniya)

2. Senegal (20)

3. Tunisia (32)

4. Algeria (33)

5. Masar (35)

6. Nijeriya (40)

7. Kamaru (43)

8. Mali (47)

9. Côte d'Ivoire (52)

10. Burkina Faso (56)

11. Ghana (60)

12. Afirka ta kudu (64)

13. Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (65)

14. Cape Verde (74)

15. Guinea (80)

16. Zambiya (81)

17. Gabon (86)

18. Uganda (90)

19. Equatorial Guinea (91)

20. Benin (93)

21. Mauritania (101)

22. Jamhuriyar Congo (106)

23. Madagascar (108)

24. Kenya (110)

25. Guinea-Bissau (110)

26. Mozambique (113)

27. Namibiya (114)

28. Angola (116)

29. Gambiya (117)

30. Togo (119)

31. Tanzaniya (121)

32. Saliyo (122)

33. Malawi (123)

34. Zimbabwe (125)

35. Libya (126)

36. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (127)

37. Comoros (128)

38. Nijar (129)

39. Sudan (130)

40. Rwanda (140)

41. Burundi (142)

42. Habasha (143)

43. Eswatini (wacce a kira da Swaziland baya) – 146

44. Botswana (148)

45. Liberiya (151)

46. Lesotho (153)

47. Sudan ta Kudu (167)

48. Mauritius (177)

49. Chadi (179)

50. Sao Tome and Principe (186)

51. Djibouti (189)

52. Seychelles (195)

53. Somaliya (196)

54. Eritrea (Ba ta da matsayi)

FIFA ta sanya jumullar kasashe 207 a duniya, inda kasar San Marino da ke kudancin Turai ta kasance a matsayi mafi karancina duniya, da maki 746.98.

TRT Afrika