Yayin da ake kawo karshen shekarar 2023, kakar kwallon kafa ta 2023/2024 manyan gasannin kasashen Turai sun cimma rabin zango. Cikin manyan gasannin biyar, an buga zangon wasanni 16 zuwa19, duk da akwai ragowar wasa guda a gasar Firmiya da za a buga a ranar karshe ta shekarar.
Ga jerin 'yan wasan da ke kan gaba a zura kwallaye a manyan gasanni biyar da suka hada da na Ingila, Sifaniya, Italiya, Jamus, da Faransa.
Kwallay 21: Harry Kane, Bundesliga
Bayan buga wasanni 16 match, dan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich kuma kyaftin din tawagar Ingila, Harry Kane ya kawar da shakkun da ake kansa, tun sanda ya sauya sheka daga gasar Firimiya. A shekararsa ta farko a gasar Bundesliga ta Jamus, yana ta samun tagomashi.
Ya ci kwallaye 21 zuwa makon wasa na 16, kuma alamu sun nuna ya fara harin cin kwallaye 40, don kamo wanda ya kafa tarihi a gasar ta Bundesliga, wato wanda ya gabace shi a Bayern, Robert Lewansdowski. Wanda ke biye masa a jadawalin cin kwallo, Serhou Guirassy na kungiyar VfB Stuttgart, kuma dan kasar Guinea ya ci kwallaye 17.
Kwallaye 18: Kylian Mbappe, Ligue 1
Tauraron kungiyar PSG ya saba cin kwallaye a gasar Ligue 1 ta Faransa, tun bayan da ya yi kaura daga Monaco a shekarar 2017. Bayan wasanni 17 a kakar bana, Kylian Mbappe ya ci kwallaye 18, kuma wanda ke bin sa Wissam Ben Yedder na kungiyar Monaco yana da kwallo 8 ne kacal.
A kungiyar Paris Saint-Germain, Mbappe ya ci kwallaye akalla 24 duk kaka, kuam da alama ba zai gaza ba a wannan kakar, inda masoya suke fatan zai haura yawan kwallayen da ya ci a bara, 30.
Kwallaye 15: Lautaro Martinez, Seria A
Yayin da kungiyoyin gasar Italiya za su buga wasansu na karshe a shekarar nan a daren yau, dan Argentinan kuma dan wasan Inter, Lautaro Martinez yana fatan yin kari kan adadin kwallaye 15 da ya ciyo wa kulob dinsa wanda ke saman tebur.
Duk da haka, shi ne zai ja ragamar cin kwallaye a Serie A a karshen shekarar nan, saboda wanda ke bi masa a jadawalin cin kwallo a gasar, wato Domenico Berardi na kungiyar Sassuolo kwallo 9 kawai yake da su, da kwantan wasa daya.
A bara ne Lautaro ya daga kofin kwallon kafa na duniya tare da Agentina, kuma yanzu yana burin karbe kyautar zakarar cin kwallo na Italiya daga hannun Victor Osimhen na Napoli. Haka nan, yana fatan ciyo wa kulon dinsa kofin Scudetto a kakar bana.
Kwallaye 14: Erling Haaland, Premier League
Duk da kafin shekar ta kare za a buga wasa na 20 na Gasar Firimiya ta Ingila, gwarzon dan wasan Manchester City Erling Haaland ba zai samu damar jefa kwallo kari kan 14 da yake da su ba, saboda raunin da ya samu. Kocinsa Pep Guardiola ya ce ba zai dawo filin wasa ba sai a karshen watan Janairu.
Dan wasan wanda dan kasar Norway ne an san shi da rashin yin sanya wajen jefa kwallo a raga, kuma ya shirya kara yawan kwallayen da yake jefawa a kakar wasanni a duk wasa.
A yayin da yake fatan lashe Kambin Gwarzon dan wasa a Firimiya a karo na biyu a jere, Haaland na fatan ka da mai biye masu a baya Mohamed Salah ko Dominic Solanke, su cimma sa kasancewar kowannensu yana da kwallaye 12 a yanzu.
Idan Solanke ya ciyo wa Bournemouth kwallaye a wasan da za su yi da Tottenham a ranar Lahadi, 31 ga Disamba, to zai iya wuce Haaland, a yayin da alkaluma ke nuna cewa dan wasan na gaba a gasar ta Ingila ya ci kwallaye 13 a kakar gasar da ta gabata.
Kwallaye 13: Jude Bellingham, La Liga
Jude Bellingham ma wani zakara ne a gasar La Liga ta Sifaniya da yake jefa kwallaye, kuma yake taka leda a Real Madrid da ke jan ragamar teburin La Liga.
Dan wasan na tsakiya dan shekara 20, ya shiga kungiyar da ke wasanni a Santiago Bernabeu ne a watan Yulin da ya gabata, kuma a yanzu yana fom yayin da ya jefa kwallaye 13 a kakar gasar bana.
Bayan buga wasanni 18 a kakar wasanni ta 2023/2024, Bellingham ya jagoranci tawagar da Carlo Ancelotti ke wa horo, wajen samun gurbin farko a La Liga inda suka yi kai-da-kai da Girona, a karshen wannan shekara ta 2023.
A yanzu da za a shiga sabuwar shekara, cikin zakarun zura kwallo guda biyar, wanda aka fi ambata a matsayin wanda zai daga tutar cin kyautar Gwarzon Zura Kwallo ta Turai shi ne Erling Haaland na Man City.
Amma game da wa zai nemi kamo Haland din, za a iya cewa ya rage na Harry Kane wanda a yanzu yake kan gaba, domin ya ga ya kai bantensa, kafin Haaland ya cimma sa.