Jorginho na Arsenal ya fara tattaunawa don komawa Palmeiras ta Brazil

Jorginho na Arsenal ya fara tattaunawa don komawa Palmeiras ta Brazil

Ɗan wasan tsakiya na Arsenal na neman barin ƙungiyar sakamakon rashin samun sabuwar kwantiragi.
Jorginho yana da shekaru 33, kuma ya zo Arsenal a Janairun 2023. / Hoto: Reuters

Rahotannin na cewa ɗan wasan tsakiyar Arsenal, Jorginho ya fara tattaunawa da ƙungiyar Palmeiras ta Brazil, domin yiwuwar komawa taka leda a can.

Ɗan wasan mai shekaru 33 ɗan asalin Italiya, yana neman barin ƙungiyar, sakamakon rashin samun sabuwar kwantiragi.

A cewar ESPN, wakilin ɗan wasan mai suna Joao Santos, ya bazama neman makoma ga Jorginho, ganin cewa kwantiraginsa a Arsenal na dab da ƙarewa a ƙarshen kakar bana.

Sai dai duk da ya fara tattaunawa da Palmeiras, ba su sanya hannu kan wata takarda a hukumance ba zuwa yanzu.

Jorginho na neman samun sabuwar ƙungiya sakamkon yadda aikinsa a Arsenal ya ragu sosai. A yanzu ƙungiyar ta Brazil ce ke burin ɗaukarsa.

Arteta na jan-ƙafa

Sai dai an kuma ce Jorginho yana kuma duba wasu ƙungiyoyin da za su buga gasar Ƙwallon Duniya ta Kulob-Kulob ta 2025, wadda za ta gudana a Amurka.

Baya ga Jorginho, rahotannin na cewa Palmeiras tana duba wani ɗan wasan tsakiya na Fulham, Andreas Pereira, kuma suna jiran amsa daga tawagar wakilansa kan yiwuwar samun sa.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya amsa cewa ya san da batun ƙaratowar kwantiragin Jorginho da abokin wasansa Thomas Partey, waɗanda za su ƙare a ƙasa da watanni shida.

Sai dai kocin ya ce yana da aniyar jinkirta tattaunawa kan tsawaita kwantiragi har sai zuwa ƙarshe-ƙarshen kakar bana.

Amma wasu majiyoyin na cewa Arsenal za ta iya bai wa Jorginho ƙarin shekara guda kacal, kamar yadda sharuɗɗansu da ɗan wasan suke a kakar bara, duk da cewa ɗan wasan ya fi son kwantiragi mai tsayi.

TRT Afrika