Jamie Vardy mai shekaru 38, ya shiga Leicester City a 2012 yana ɗan shekara 25. / Hoto: AP

Shahararren ɗan wasan gaba na Leicester City, Jamie Vardy ya kafa sabon tarihi a ƙungiyarsa, bayan ya ci ƙwallo a wasan da suka buga da Tottenham a ƙarshen makon jiya.

Ƙwallon da ya ci a zagaye na biyu na wasan ta taimaka wa ƙungiyar inda ta ƙara ƙwallo ta biyu sannan ta yi nasara aka tashi wasan da ci 2-1.

Bayan cin ƙwallon, Vardy ya durfafi ɓangaren masoyan Leicester inda ya ringa alamta lamba ɗaya, yana nuna tambarin Firimiya da ke kafaɗarsa, sannan ya alamta sifiri yana nuna masoya Tottenham.

Vardy ya yi hakan ne don tuna wa 'yan kallo cewa Leicester ta taɓa lashe kofin Firimiya sau ɗaya a 2015-16, yana mai zolayar Tottenham, wadda ba ta taɓa ɗaga kofin na Firimiya ba.

Jamie Vardy ya shiga sahun zaratan 'yan wasan irinsu Cristiano Ronaldo, Ryan Giggs, da Teddy Sheringham wajen ba da tallafin ƙwallaye 10 zuwa sama yayin da suke masu shekaru 37 ko sama da haka.

A wannan kakar ta 2024-25, Vardy wanda tsohon ɗan wasan tagawar Ingila ne ta Three Lions, ya ci ƙwallaye bakwai, da kuma tallafin ƙwallaye uku a wasanni 21 da ya buga.

Ƙarƙashin sabon koci Ruud van Nistelrooy, Leicester City tana mataki na 17 da maki 17, bayan wasanni 23. Za ta buga wasa na gaba ranar 1 ga Fabrairu tare da Everton a gasar Firimiya.

TRT Afrika