Rahotannin daga Real Madrid na cewa haziƙin ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Vinicius Jr ya ƙi amincewa da tayin tsawaita kwantiraginsa a Madrid, kuma har ya fara tattaunawa da PSG ta Faransa.
Wata tawaga daga PSG ta yi tattaunawa kan yiwuwar ɗauko Vinicius, bayan ya yi watsi da tattaunawa da hukumomin Madrid kan sanya hannu a sabuwar kwantiragi a Sifaniya.
Makonni biyu da suka wuce ne aka yi wata zantawa kan kwantiragi tsakanin Real Madrid da Vinicius, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Sai dai ba a cim ma matsaya ba.
Ɗan wasan ɗan asalin Brazil ya ƙi amsa tayin ne saboda ya yi tsammanin samun ƙarin kuɗi daga Madrid, saboda imaninsa na cewa darajarsa ta haura abin da aka masa tayi.
Baya ga batun na PSG, akwai wasu raɗe-raɗin da ke cewa ba daɗewa ma Vini ya samu tayi daga jami'an ƙwallo na Saudiyya, inda aka ce an yi tayin ba shi kwantiragin da za ta kai euro biliyan guda a shekara biyar.
Wannan tayi ne aka ce ya sanya Vini ya sake tunanin kan tsawaita zamansa a Real Madrid.
Turai ko Saudiyya?
Rahotannin sun ambato shafin Sky Sports na cewa PSG sun yi tattaunawar share-fage da wakilan Vinicius, kuma za su zuba ido don ganin ko Madrid za ta gaza cika burin Vini, inda za su miƙa nasu tayin.
Duk da cewa Vinicius na da kwantiragi da Madrid da ba za ta ƙare ba har sai Yunin 2027, wakilansa sun nuna ƙarara cewa zamansa a can ba shi da tabbas, face Madrid ta ba shi kimar da ta dace da shi.
A hakan, Ma'aikatar Wasanni ta Saudiyya ta ci gaba da tuntuɓar wakilan ɗan wasan, kuma suna ƙarfafa batun komawarsa can a matsayin abin da suke kyautata yiwuwarsa.
Tuni wasa jaridun Sifaniya suke gulmar cewa akwai takun-saƙa tsakanin 'yan wasan Madrid da Vinicius.
Wasu rahotannin sun yi iƙirarin cewa manyan 'yan wasa ciki har da Luka Modric suna jin haushin gazawar Vini wajen kare gida, da salonsa na neman faɗa a fili, da yawan jayayya da alƙalan wasa.
Wannan zarge-zarge suna nuna cewa wasu 'yan wasan ba za su ƙi zaɓin sayar da Vinicius ba, musamman ganin tayin albashin da aka yi masa, wanda ya kai euro miliyan €300 daga Saudiyya.
Kyakkyawar dama
Sai dai duk da gwaggwaɓan tayi daga PSG da Saudiyya, har yanzu Real Madrid na da kyakkyawar damar riƙe Vinicius Jr.
Shugaban Real Madrid, Florentino Perez yana kallon ɗan wasan a matsayin wani ginshiƙin tawagarsa. Don haka ana ganin yiwuwar cewa sabuwar kwantiragi na tafe ga ɗan wasan.
Yayin da ake tababa kan makomar Vinicius Jr, ɗan wasan zai mai da hankali kan taimaka wa Madrid a wasansu na gasar Zakarun Turai da za su yi da Manchester City a maraicen yau.
Wasan yana da matuƙar muhimmanci saboda suna mataki na 'yan-16, inda nasararsu za ta ba Vini damar ci gaba da nuna ƙwazonsa a ƙungiyar, da kuma damar sake lashe kofin Turai kamar yadda suka yi a bara.