Tawagar Senegal ta "Zakunan Teranga" su ke riƙe da kofin gasar CHAN. / Hoto: CAF

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙara adadin kuɗin da ake bai wa ƙasashen da suka yi nasara a gasar da hukumar ke tsarawa, wadda za ta gudana a Kenya da Tanzania da Uganda a shekarar nan.

A cewar sanarwar hukumar CAF, ƙarin ya kai kashi 75% cikin 100, inda ƙasar da ta yi nasarar ɗaga kofin za ta samu zunzurutun kuɗi dala miliyan 3.5.

CAF ta sanar da cewa an ƙara jimillar kuɗaɗen da za a bayar ga ƙasashen da suka yi zarra a gasar da kashi 32% (zuwa dala miliyan $10.4).

A sanarwar, shugaban CAF Patrice Motsepe, ya ce gasar “wani ɓangare ne na dabarun zuba jari a harkar ƙwallon Afirka, da mayar da ita mai jan hankli da ba da sha'awa ga masoya, da masu kallo a talabijin, da masu ɗaukar nauyi, da abokan haɗin gwiwa, da sauran masu ruwa da tsaki da ke Afirka da duniya baki ɗaya.”

Gasar da da za a yi a Kenya, Tanzania, da Uganda an shirya za ta fara daga 1 zuwa 28 ga Fabrairun 2025.

Ƙasashen da suka cancanta

Ƙasashe 17 sun samu shiga gasar, wato Kenya, Tanzania, Uganda, Morocco, Guinea, Senegal, Mauritania, Nijar, Burkina Faso, Nijeriya, Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, Congo, Sudan, Zambia, Angola, da Madagascar.

Sanarwar ta CAF ta ce, “Gasar CHAN muhimmiyar gasa ce don cigaba da kuma haɓakar 'yan ƙwallo da suke taka leda cikin nahiyar Afirka, da matasan da ke tallafa wa harkar ƙwallo a duniya da kuma gasannin CAF.”

A gasar CHAN ta ƙarshe da aka yi a 2022, tawagar Senegal ta "Zakunan Teranga" ta lashe kofin bayan ta doke tawagar mai masaukin baƙi Algeria, da ci 5-4 a bugun ɗurme da aka yi a wasan ƙarshe.

TRT Afrika