Gabanin buga wasan da Man City za ta yi da Burnley, kocin City, Pep Guardiola ya bayar da sabbin bayanai kan lafiyar babban dan wasansu, Erling Haaland.
Guardiola ya bayyana cewa Haaland zai dawo cikin tawagar farko ta kungiyar, bayan da ya murmure daga jinyar da ya tafi tun watan Disamba.
Haaland ya yi jinyar sama da wata guda sakamakon raunin da ya samu a kafarsa a wasansu da Aston Villa, wanda tun bayan nan bai samu sauki ba.
A jawabin da ya yi na kafin wasan City na wannan Laraba, Guardiola ya tattauna da 'yan jarida inda ya bayyana cewa 'yan wasansu biyu ne za su dawo wasa a wannan makon.
Guardiola ya ce, "Yanzu muna da cikakken adadi na 'yan wasa, kuma Haaland muhimmin dan wasa ne gare mu".
Dayan dan wasan shi ne Manuel Akanji wanda shi ma bai buga wasa ba na dan lokaci a kwanakin baya. Haka nan babu fargaba kan lafiyar dan wasan baya John Stone.
A yanzu dai, kocin Man CIty yana da zabin amfani da kowane dan wasa da ke cikin tawagarsa, bayan dawowan mutum biyun daga jinya.
Man City dai tana mataki na biyu a teburin Firimiya da maki 43, inda Liverpool ke gabanta da maki 48, duk da cewa City tana da kwantan wasa guda da ba ta buga ba.