Manchester City wadda ke riƙe da kofin FA na bara, za ta haɗu da Chelsea a wasan kusa da na ƙarshe wanda za a buga a Wembley, a ranar 20 ga watan Afrilu mai zuwa.
Ita kuma Manchester United, wadda a yammacin Lahadi ta fitar da Liverpool daga gasar ta FA, za ta kara da ƙungiyar Coventry, wadda ke buga wasa a ƙaramin matakin ƙasa da na Firimiya.
Wannan jadawalin wasannin kusa da na ƙarshe na gasar, ya sa yanzu akwai yiwuwar a sake maimaita abin da ya faru a bara, inda ƙungiyoyi biyu na garin Manchester suka kece raini a wasan ƙarashe na gasar FA.
A bara dai, Man City ce ta doke Man united da ci 2-1, wanda ya ba ta damar cin kofuna har uku a kakar ta bara.
A bana ma City na burin cin kofuna uku, wato kofin Fa, da kofin Firimiya inda take mataki na biyu a yanzu, da kuma kofin Zakarun Turai, inda take matakin kwata-fainal.
Yayin da a ranar Asabar, cikin sauƙi Man City ta lallasa ƙungiyar Newcastle da 2-0, Chelsea kuwa sai da ta kai mintunan ƙarshe na wasansu da Leicester, kafin su doke su da 4-2 a filin wasa na Stamford Bridge.
Ita ma Man United da da gumin goshi ta samu ta doke Liverpool a wasansu na Lahadi, bayan da sau biyu ana ba su tazarar ci 2-1 a kashin farko na wasan, da kuma ci 3-2 a kashin ƙarshe na wasan.
A ƙarshe ne United ta samu galaba bayan da ɗan wasansu Amad Diallo, ɗan asalin Ivory Coast, ya ci musu a ƙwallo ta huɗu, inda aka tashi 4-3 a filin wasa na Old Trafford.
Man United ta fitar da Liverpool, wadda a yanzu kofuna uku suka rage mata damar lashewa, a wannan kakar da ita ce karo na ƙarshe da koci Jurgen Klopp zai jagoranci ƙungiyar.
Ana kyautata zaton Man United ce za ta yi nasara kan Coventry, inda za ta haɗu da ko dai Man City ko Chelsea a wasan ƙarshe da za a buga a babban filin wasa na Ingila, wato Wembley.