Ɗan wasan Manchester City ɗan asalin Ingila, Phil Foden ya doke abokin wasansa a City, Erling Haaland wajen cin kyautar gwarzon shekara na ƙungiyar PFA ta bana.
Ranar Talata ne Ƙungiyar Ƙwararrun 'Yan Ƙwallon Ƙafa ta Ingila, PFA ta ba da kyautar gwarzon ɗan wasa ga ɗan wasan mai shekaru 24, wanda ya ci ƙwallaye 27 a wasanni 53 da ya buga a bara a duka gasanni.
Foden ya taimaka wa City lashe kofin Firimiya na huɗu a jere, tare da gwarzon abokin wasansa, Erling Haaland wanda a bara shi ne ya ci kyautar.
Shi ma tsohon ɗan wasan City, kuma ɗan wasan Chelsea a yanzu, Cole Palmer ya ci kyautar matashin gwarzon ɗan wasan na bana na ƙungiyar ta PFA.
Palmer wanda yake da shekaru 22, ya ci ƙwallaye 22 a wasanni 34 na gasar Firimiya a kakarsa ta farko a Chelsea, bayan ya bar Man City a 2023 kan kuɗi Fam miliyan £42.5 (dala miliyan $55).
A Chelsea, Palmer ya zamo cikin mafi kyawun ɗan wasan da suka ɗauko, inda ya taɓa cin ƙwallaye uku a wasansu da Manchester United a Afrilu, kuma ya ci ƙwallaye huɗu a wasa guda a wasansu da Everton.
Shafin Goal.com ya ruwaito Foden yana cewa, "Lashe wannan kyauta abu ne mai matuƙar muhimmanci gare ni. Ina alfahari kuma ina godiya."
Foden da Palmer sun buga wa tawagar ƙasar Ingila a gasar Euro 2024 ta bana da aka buga a Jamus, inda suka kai tawagarsu zuwa wasan ƙarshe kafin tawagar Sifaniya ta doke su ta lashe kofin.