FIFA ta ce za ta nemi shawarar masana shari'a don duba buƙatu uku na Falasɗinu. / Hoto: DPA

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA za ta nemi shawarar masana shari'a masu zaman kansu kafin gudanar da taro na musamman na baban zauren gudanarwarta ranar 25 ga watan Yuli, don ɗaukar mataki kan buƙatar Falasɗinawa don neman dakatar da Isra'ila daga ƙwallon duniya saboda take haƙƙin ɗan-adam a Falasɗinu.

Shugaban FIFA Gianni Infantino ya fitar da wani shiri a taron FIFA ranar Juma'a bayan da wakilan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu da na Isra'ila suka samu damar magana gaban hukomomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 211 da ke mambobin FIFA.

Infantino ya ce, “FIFA za ta nemi a yanzu, ƙwararre kan shari'a mai zaman kansa ya yi biyar buƙatun (daga Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu) kuma ta tabbatar an zartar da dokokin FIFA yadda ya dace”.

“Wannan bita ta shari'a za ta ba da damar jin ta bakin mambobin biyu da hukumomin ƙwallon ƙafa na Falasɗinu da na Isra'ila. Sakamakonsu da shawarwarinsu ... za a miƙa wa zauren hukumar FIFA.

Lalata gine-gine a Gaza

“Saboda buƙatar gaggawa a batun, taro na musamman na Zauren FIFA zai haɗu don ya ɗauki mataki kafin 25 ga Yuli, don duba sakamakon bitar shari'ar domin ɗaukar matakan da suka dace.”

Ƙorafin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu ta gabatar ya nuni da, “Taka dokar ƙasa-da-ƙasa da Isra'ila ta aikata sakamakon mamayar Falasɗinu, musamman a Gaza” kuma ya ayyana dokar FIFA mai kare haƙƙin ɗan-adam da hana wariya.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu ta rubuta cewa, “duka gine-ginen ƙwallon ƙafa a Gaza ko dai an lalata su, ko an lahanta su sosai, har da filin wasa mai ɗimbin tarihi na Al Yarmuk” kuma ya ce ta samu goyon baya ga buƙatunsu daga hukomomin ƙwallon ƙafa na Algeriya, da Iraq, da Jordan, da Syria da Yemen.

TRT Afrika