Kocin Manchester United, Erik ten Hag, ya ce dole yaransa su matsa kaimi don tabbatar da cewar damar shiga gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa ba ta zille musu ba.
Da yake magana da manema labarai bayan Spurs ta rike Man U da ci 2-2, Ten Hag ya ce dole su zage dantse wajen tabbatar da cewa ba su sake barar da maki a gasar Firimiya ba.
"Muna da sauran wasanni. Muna bukatar ci gaba da tafiya kuma mu sake yarda da kanmu don mu karasa (kasancewa cikin masu zuwa gasar Zakarun Turai)," a cewar kocin na Man United.
Kungiyoyin da suke mataki na daya zuwa na hudu a gasar Firimiyar Ingila ne za su wakilci kasar a gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa.
United ce ta hudu a gasar Firimiya a halin yanzu inda take da maki 60, yayin da Tottenham ke da 54 da Aston Villa (54) da kuma Liverpool (53).
Canjaras din da United ta yi da Tottenham ya sa ta barar da maki biyu, kuma idan ta cigaba da haka daya daga cikin kungiyoyin da ke bin ta a teburin Firimiya za ta iya kwace gurbin shiga gasar ta Zakarun Turai daga hannunta.
Wannan ne ya sa kocin Man U yake cewa yaransa za su cigaba da mayar da hankali 100 bisa 100 kan wasannin da suka rage a wannan kakar don ci gaba da rike damar shiga gasar Zakarun Turai.
Man United na da karawa da Aston Villa da Brighton da West Ham da Wolves da Bounemouth da Chelsea da kuma Fulham kafin gasar Firimiya ta kakar bana ta kare.
Kuma Kocin Man United na son yaransa su yi nasara a wasannin don tabbatar da damarsu ta shiga gasar zakarun Turai.