Declan Rice ya doke 'yan wasa da dama na gasar Firimiya. / Hoto:  London Football Awards

An bayyana ɗan wasan Ingila da Arsenal, Declan Rice a matsayin Gwarzon Ɗan Wasan Gasar Firimiya na Shekara a wajen bikin London Football Awards na 2024.

Declan Rice ya doke manyan ƴan wasa a gasar Firimiya inda ya ci kyautar London Football Awards. Ƴan wasan sun haɗa da abokin wasansa a Arsenal William Saliba, da Jarrod Bowen na West Ham, Guglielmo Vicario da Pedro Porro na Tottenham Hotspur.

Tun bayan da Arsenal ta saye shi a 2023 a kan kusan fam miliyan 105 (dala miliyan 132.6), Declan Rice ya nuna bajinta inda ya ci ƙwallaye huɗu ya kuma taimaka aka ci ƙwallaye shida da suka bai wa Arsenal damar shigewa a gaba a neman cin kofin Firimiya.

Declan Rice ya ce yana alfahari da buga wa Arsenal wasa. / Hoto: London Football Awards

Da yake jawabin godiya bayan amsar kyautar, Declan Rice ya ce, “Tawagarmu ta koyi darusa da dama a bara. Mun ƙara ƙarfi da imani. Idan aka ci mu ƙwallo ɗaya, muna da ƙwarin gwiwa za mu farke. Ina matuƙar alfahari da kulub ɗina”.

An yi bikin ne ranar Alhamis da daddare a Camden Roundhouse, a inda babban kocin Tottenham, Ange Postecoglou ya ci gasar gwarzon manaja na shekara.

Kocin, wanda ɗan Australia ne, ya doke manajan Arsenal Mikel Arteta wanda shi ma ya yi takara, saboda ya kawo ci-gaba a Spurs tun bayan da ya karɓi ragamar kulob ɗin a bazarar bara inda a yanzu yake neman cancantar shiga gasar Zakarun Turai.

Cole Palmer na Chelsea ya ci kyautar matashin dan wasa na shekara a bikin. / Hoto: London Football Awards

Kazalika an karrama Cole Palmer na Chelsea a matsayin gwarzon matashin ɗan wasan Firimiya, wanda ya ci ƙwallaye 14 a wasanni 32 tun bayan zuwansa daga Man City a kan fam miliyan 40 (dala miliyan 50.5) a bara.

Chelsea ta samu ƙarin masu cin kyauta a bikin, inda Lauren James ta ci Gwarzuwar ƴar wasan mata ta shekara ta Super League, inda Aggie Beever-Jones ta ci kyautar Matshiyar ƴar wasa ta shekara.

TRT Afrika