A halin yanzu dai Arsernal tana gaban Liverpool ne da yawan ƙwallaye inda ta buga wasanni 31 yayin da Liverpool ta buga wasanni 32./Hoto:Reuters

Crystal Palace ta jika wa Liverpool aiki bayan ta tsuke damarta ta cin gasar Firimiya inda ta doke ta da ci daya da nema a karawar da suka yi a Anfield, gidan Liverpool.

Wannan sakamakon ya hana Liverpool mai maki 71 hayewa teburin gasar Firimiya inda take ta uku a bayan Manchester City wadda take da maki 73 da kuma Asernal mai maki 71.

A halin yanzu dai Arsernal tana gaban Liverpool ne da yawan ƙwallaye inda ta buga wasanni 31 yayin da Liverpool ta buga wasanni 32.

Arsernal za ta iya hayewa teburin gasar a wasan da za su yi anjima da Aston Villa idan ta samu ta doke ƙungiyar Villa wadda Unai Emery tsohon kocin Arsenal ke jagoranta.

Bayan wasannin yau, ƙungiyoyi uku da ke saman teburin gasar Firimiyar suna da wasanni shida da za su buga kafin a ƙarƙare gasar Firimiya ta kakar bana.

Wasu na ganin sakamakon wasan yau ya nuna cewa Manchester City da Arsernal ne suke da damar lashe gasar Firimiya a kakar bana yayin da wasu ke ganin ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.

TRT Afrika da abokan hulda