'Yan wasan ƙwallo 10 da ke kangaba suna samun jimillar dala miliyan $983 a kakar bana. / Hoto: Reuters

Mujallar Forbes ta sabunta jerin 'yan wasan ƙwallon ƙafa da suka fi kowa samun kuɗi a duniya, a shekarar 2024, inda shaharrarren ɗan wasa ɗan asalin Portugal, Cristiano Ronaldo wanda ke buga wasa a Al Nassr ta Saudiyya ke kangaba.

Ronaldo ya koma ƙungiyar Al Nassr a Janairun 2023, kuma shi ne kan gaba a karo na shida, inda yake samun ƙiyasin dala miliyan $285 a bana (sama da dala miliyan $260 da ya samu a 2023), wato dala miliyan $220 a filin wasa, da dala miliyan $65 a wajen fili.

Lionel Messi ne na 2 da ƙiyasin kuɗin da ya kai dala miliyan $135, inda yake samun dala miliyan $75 a wajen fili. Sai na 3, Neymar Jr na Al Hilal ta Saudiyya, da dala miliyan $110, mai samun dala miliyan $80 a fili, da miliyan $30 a wajen fili.

Saudiyya ce kangaba

Karim Benzema na Al Ittihad ne na 4, da dala miliyan $104, inda yake samun miliyan $100 a fili da miliyan $4 a wajen fili. Sai Kylian Mbappe na real Madrid a mataki na 5, da dala miliyan $90, miliyan $70 a fili, da miliyan $20 a waje.

Erling Haaland na Manchester City shi ne na 6 da dala miliyan $60, sai Vinicius Jr na Real Madrid a mataki na 7, da dala miliyan $40. Mohamed Salah na Liverpool yana mataki na 8, da dala miliyan $53.

Sadio Mane wanda shi ma yake taka leda a Al Nassr, shi ne a mataki na 9, da dala miliyan $52, inda yake samun dala miliyan $48 a fili da miliyan $4 a waje. Sai kuma Kevin De Bruyne na Man City a mataki na 10.

A wannan bazarar kawai ƙungiyoyin ƙwallo na Saudiyya sun kashe dala miliyan $524 wajen sayayyar 'yan wasa, kamar su Moussa Diaby, Ivan Toney, da Marcos Leonardo.

Hanyar samun kuɗi

'Yan wasan dai suna samun kuɗi ne ta albashi, da yin talla, da kuma abubuwan da eke sayarwa ɗauke da suna ko hotonsu, da ma sauran hanyoyin samun kuɗi.

Ƙasar Saudiyya inda ake buga gasar Saudi Pro League ita ke kangaba a yawan 'yann wasan da ke sahun mutane 10 mafi samun kuɗi a harkar ƙwallo a duniya, inda suke da mutum huɗu.

Baya ga gasar Saudiyya, gasar Firmiya ta Ingila ce ke bi mata baya, da 'yan wasa guda uku, sai LaLiga ta Sifaniya mai 'yan wasa biyu, sai gasar MLS mai ɗan wasa guda.

TRT Afrika