Federico Chiesa ɗan asalin Italiya, kuma gwarzon ɗan wasan Juventus ta Italiya, ya zo Liverpool a bazarar bara, amma tauraruwarsa ba ta haska ba zuwa yanzu.
A yanzu ɗan wasan yana neman barin Liverpool a Janairun nan don ya koma Italiya, ganin cewa mintuna 123 kawai ya buga zuwa yanzu, tun bayan zuwansa ƙungiyar a bazarar bara.
Rahotanni na cewa akwai ƙungiyoyi masu sha'awar ɗaukar sa a Serie A, cikinsu har da AC Milan da Napoli da Roma.
Ya bar Juventus a bazarar 2024 ne bayan ƙaratowar ƙarshen kwantiraginsa a ƙungiyar, sannan ya yi ta samun raunuka da tafiya jinya.
Chiesa wanda ya lashe gasar Euro 2020 tare da tawagar Italiya, ya bar ƙasarsa inda ya zo Liverpool kan farashi mai rangwame na dala miliyan $12m kacal.
Mai shekaru 27, Chiesa bai samu tagomashi a Liverool ba, kuma kocinsa Arne Slot bai gamsu da ƙoƙarinsa ba don haka ba ya saka shi wasa a-kai-a-kai.
Chiesa ya buga babban wasa ne guda kawai, kuma sau ɗaya aka fara wasa da shi a gasar kocin Carabao, wanda Liverpool ta doke West Ham da ci 5-1 a Satumban 2024.
Wasanni huɗu
Uku cikin wasanni huɗu da Chiesa ya buga a watan na Satumba ne, kuma tun 18 ga Disamba rabonsa da buga wasa.
An ruwaito koci Slot yana faɗa game da Chiesa, "Idan ɗan wasa bai buga wasa ba tsawon watanni biyar ko shida, ba za ka sa ran ya yi ƙwazo kai-tsaye ba.
A yanzu shafin Goal ya ambato mujallar Footmercato na cewa Chiesa yana neman sauyin ƙungiya a Janairun nan.
Ana sa ran zai tafi aro na gajeren lokaci saboda ƙungiyoyi a Italiya suna jan ƙafa kan biyan sa ko da rabin albashinsa na dala miliyan $8 duk shekara.
Duk da ɗan wasan gwani ne a kai farmaki, samun dama a Liverpool za ta ci gaba da masa wahala kasancewar akwai gwaraza irinsu Mohamed Salah, Cody Gakpo, Diogo Jota, Darwin Nunez, da Luis Diaz a gabansa.