Hukumomin ƙungiyar Chelsea ta Ingila sun koka kan yadda mutane a soshiyal midiya suke muzanta launin fatar ɗan wasansu Nicolas Jackson, tun bayan wasan da suka sha kaye a hannun Manchester City a gasar FA.
Chelsea ta bayyana cewa, "Mun ji takaici kan zagin launin fatar da ake wa Nicolas Jackson ta kafofin sada zumunta na zamani", bayan wasan da Man City ta doke Chelsea a matakin dab da na ƙarshe na gasar FA ranar Asabar.
A wannan wasan ne Nicolas Jackson ya ɓarar da aƙalla damarmaki uku da ake gani zai iya zura ƙwallo. Rashin cin ƙwallon ya ba wa Man City damar yin nasara a wasan, bayan suka zura ƙwallo ɗaya tilo a minti na 84.
Chelsea ta faɗa a wata sanarwa cewa, "Ba za mu taɓa amincewa da duk nau'in wariya ba a al'ummarmu, kuma muna aiki kan tsarin ƙin laminta duk irin wannan hali".
"Kulob ɗinmu zai goyi bayan duk wata shari'a kan batun, kuma za mu ɗauki tsattsauran mataki, wanda zai ƙunshi haramci kan duk wani mai laifi da aka gano yana da tikitin shiga filin wasanmu na kaka guda, ko kuma mambanmu ne."
Nicolas Jackson, ɗan shekara 22 wanda ɗan asalin Senegal ne ya zo Chelsea a watan Yulin 2023, daga ƙungiyar Villareal ta Sifaniya kan kuɗi Fam miliyan 35, da kwantiragin shekara takwas. A wannan kakar ya ci ƙwallaye 13, 10 cikinsu a gasar Firimiya.
Kocin Chelsea Mauricio Pochettino ya ce game da Nicolas, "Shi babban ɗan wasanmu ne na gaba, kuma shi kaɗai ne sitiraikanmu da ke da ƙoshin lafiya".
"Yana ƙoƙari sosai. Yana aiki da bajinta ga tawagarmu; yana da kuzarin gudu, da cin ƙwallo, da tallafawa cin ƙwallo. Karonsa na farko a matsayinsa na matashi ya fara ne a Sifaniya, duk da ba shi da ƙwarewa mai yawa a can", in ji Pochettino.
Pochettino ya ƙara da cewa, Nicolas "yana buƙatar ƙarin lokaci don ya haɓaka wasansa. Tabbas zai nuna ƙarin hazaƙa a kakar baɗi, ba ni da tantama kan wannan".