Shirin cefanar da Manchester United ya shiga zagaye na gaba, inda ake sa ran hamshakan masu kudin nan guda biyu, Sheikh Jassim dan kasar Qatar, da Sir Jim Ratcliffe za su yi tayinsu na uku.
Jaridar Express ta Birtaniya ta ambato wasu rahotanni masu nuna cewa wadanda ke yunkurin sayen kulob din sun ji takaicin rashin cigaban da aka samu daga mamallaka kulob din na yanzu, wato iyalan Glazers, tun bayan mika tayin a zagaye na biyu.
Iyalan na Glazers, wadanda suka mallaki kaso mafi tsoka na hannun jarin United, sun nemi masu son sayen kulob din da su sake aiko da tayi a karo na uku.
Ta bayyana cewa mamallaka kulob din ba su gamsu da tayin da suka samu ba zuwa yanzu, domin kuwa suna da burin farashin kulob din ya kai fam biliyan 5.
Alamu sun nuna Iyalan Glazers suna duba yiwuwar siyar da kulob din ga wadanda ke burin mallakar wani kaso na hannun jarinsa, maimakon sakin gabadaya kulob din. Sai dai wasu rahotannin sun nuna cewa kawunan iyalan ya rabu game da wannan zabi.
Kamfanin Raine Group, wanda aka dora wa alhakin cefanar da kulob din, ya ba da wa'adin karshen watan Afrilu, don karbar sabbin tayi. Ana ganin za a samu tayi daga bangarori har bakwai.
Amma an fi sa ran manyan masu neman siyan kulob din su biyu za su aiko da tayinsu, wato Sheikh Jassim da kuma Sir Jim Ratcliffe.
A halin da ake ciki dai, kulob din na United da ke karkashin jagorancin Erik ten Hag, yana mataki na hudu a teburin gasar Firimiya, inda ake sa ran zai samu buga wasan Zakarun Turai a badi.
Sannan kulob din zai buga wasa na gaba a gasar Europa tare da kungiyar Sevilla ta Sifaniya ranar Alhamis, yayin da kuma yake mataki na daf da na karshe a gasar FA ta Ingila.