Ƙasar Ivory Coast ce ke riƙe da kofin gasar AFCON a halin yanzu. / Hoto: Getty

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta ƙaryata rahotannin da ke yawo, kan cewa an ɗage gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON, wanda aka tsara yi a shekarar 2025, da watanni shida.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, hukumar CAF ta bayyana labarin a matsayin ''ƙarya'', kuma wanda ba shi da tushe.

"Sanarwa game da yiwuwar ɗage gasar AFCON na 2025 ƙarya ne, sannan kwamitin zartarwa na CAF zai gana don tattaunawa tare da yanke shawara kan ranakun gasar a 2025, '' in ji CAF, a cikin wata gajeriyar sanarwar da ta wallafa a X.

Rahotannin dai sun bayyana cewa an sauya lokacin gasar, wadda ƙasar Maroko za ta karɓi baƙunci, inda aka matsar da shi zuwa shekarar 2026.

Ƙiki-kaka kan tsarin jadawalin gasar

Tantamar ta samo asali ne daga tsarin jadawalin lokacin da 'yan wasa wadanɗa ke taka leda a manyan ƙungiyoyinsu mabambanta za su yi na tsawon kakar wasa, kana su buga gasar cin kofin kulob na duniya daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga Yuli na 2025, sannan su kuma dawowa su buga gasar CAF da za a yi a gaba.

''Shin hakan zai dace da buƙatun 'yan wasan?'' cewar sakatare janar na hukumar CAF, Veron Mosengo-Omba a wata hira da kafar yaɗa labarai ta BBC.

Ko da yake dai hukumar CAF ta ce za a '"fitar da sanarwa a hukumance kan batun", bayan tattaunawar.

Kazalika, hukumar na fuskantar matsin-lamba kan ta tsayar da ranakun da za a buga wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka, a fannin mata na bana, wanda shi ma ƙasar Maroko ce mai masaukin baƙi.

TRT Afrika da abokan hulda