'Yan Nijeriya Victor Osimhen da Asisat Oshoala sun lashe kyautar gwarazan 'yan kwallon Afirka na CAF 2023./Hoto: CAF

'Yan Nijeriya Victor Osimhen da Asisat Oshoala sun lashe kyautar gwarazan 'yan kwallon Afirka na CAF 2023 a rukunin maza da mata a bikin da aka gudanar a Marrakech, babban birnin Maroko ranar Litinin da maraice.

Osimhen, wanda yanzu shi ne zakaran kwallon kafar Italiya, ya doke dan wasan Liverpool da Masar Mohamed Salah da dan wasan Paris Saint-Germain da Maroko Achraf Hakimi inda ya lashe kyautar.

Oshoala, mai shekara 29, tana cikn 'yan wasan Nijeriya mata da suka kai zagayen 'yan-goma-sha-shida a Gasar Kwallon Kafa ta FIFA da aka gudanar a bazara a kasashen Australia da New Zealand ko da yake Ingila ta fitar da su daga gasar.

Ta zama 'yar kwallon kafar Afirka ta farko da ta ci wasa a Gasar cin Kofin Duniya uku, a 2015 da 2019 da kuma bana.

Ga jerin sauran rukunan da suka samu nasara a wajen bayar da kyautar:

Gwarzuwar tawagar kwallon kafa ta kasa a rukunin maza - Maroko

Gwarzuwar tawagar kwallon kafa ta kasa a rukunin mata – Nijeriya

Gwarzon matashin dan wasa na shekara - Lamine Camira – Senegal

Gwarzuwar matashiyar 'yar wasa ta shekara - Nesryne El Chad - Maroko

Kulob da ya fi bajinta a shekara - Al Ahly - Egypt

TRT Afrika