Borussia Dortmund ta kori kocinta Nuri Sahin, bayan da sabuwar shekarar nan ta ƙi yi wa ƙungiyar daɗi, inda ta yi rashin nasara a wasanni huɗu cikin 5 da ta buga a baya-bayan nan.
A ranar Laraba ne Dortmund ta sanar da korar kocin mai shekaru 36 ɗan asalin Jamus mai tsatso a Turkiyya, kwana guda bayan da suka sha kaye da ci 2-1 a hannun Bologna a gasar Zakarun Turai mako na 7.
Wannan rashin nasara ita ce ta huɗu a wannan shekara, kuma ta mayar da ƙungiyar zuwa mataki na 13 a gasar da ta ƙunshi ƙungiyoyi 36. Haka nan Dortmund tana mataki na 10 ne da maki 25 a gasar Bundesliga, bayan wasanni 18.
Daraktan wasanni na ƙungiyar, Lars Ricken, ya faɗa a wata sanarwa cewa, “Muna matuƙar girmama Nuri Sahin da aikinsa, kuma mun so mu yi aiki da shi tsawon lokaci kafin yanzu".
"Bayan shan kaye sau 4 a jere, da nasara a wasa ɗaya kacal cikin wasanni 9 na baya-baya nan, da kasancewa a mataki na 10 a Bundesliga, muna baƙin cikin cewa mun cire tsammani kan cimma manufarmu ta wasa a wannan yanayi.
"Wannan mataki ya min ciwo ni kaina, amma ba za mu iya kaucewa hakan ba bayan wasanmu da Bologna."
Kocin riƙo
A yanzu dai kocin 'yan ƙasa da shekaru 19 na ƙungiyar, Mike Tullberg shi zai karɓi ragama a wasan Dortmund na gaba da Werder Bremen, a gasar Bundesliga ranar Asabar. Amma ba a ambaci wa zai zama koci na dindindin ba.
A watan Yunin da ya gabata ne Nuri Sahin ya karɓi aiki bayan da a baya yake mataimakin tsohon koci Edin Terzic, wanda ya ajiye aiki bayan Dortmund ta sha kaye da ci 2-0 a hannun Real Madrid a wasan ƙarshe na Zakarun Turai na bara.
A wasansu da Bologna, an ga ɗan wasansu Serhou Guirassy ya yi murnar cin ƙwallo tare da Sahin, a wani abu da aka kalla a matsayin nuna goyon baya. Sai dai an ci Dortmund ƙwallo 2 a mintuna 2, sannan aka tashi da 2-1.
Nuri Sahin yana da masoya a Dortmund tun sanda yana buga wasa, bayan ya shiga ƙungiyar yana matashi a 2001, kafin ya koma Real Madrid bayan shekara 10. Sannan ya sake dawowa Dortmund a karo na biyu a 2013 zuwa 2018.
Sai dai kafin aiki a Dortmund, Sahin ba shi da tarihin horar da wata babbar ƙungiya idan ban da riƙe ƙungiyar Antalyaspor ta Turkiyya.